An ɗaure wani matashi da yayi ma wani mutum ƙwakƙwaran naushi har ta mutu
Wata kotun majistri dake jihar Osun ta bada umarnin daure mata wani matashi mai shekaru 21, Sodiq Adewale kan zarginsa da aikata laifin kisan kai, inji rahoton kamfanin dillancin labaru.
Da fari dai dansanda ma kar ya shaida ma kotu cewar matashin ya tafka wannan aika aika ne a ranar 30 ga watan Nuwamba da misalin karfe 10 na safe a cikin jami’ar Obafemi-Awolowo, inda ya naushi wani mai suna Omoboriowo Olufemi, nan take ta ce ga garinku nan.
KU KARANTA: Wani malalacin Maigida ya gamu da fushin Uwargida, ta kwance masa zani cikin kasuwa
Dansandan yace wannan laifi ya saba ma sashi na 316 (1) da 319 (1) na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Osun, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Sai dai a zaman sauraron karar na karshe daya gudana a ranar Talata 12 ga watan Disamba, alkali Risikat Olayemi ta bayyana cewa bata da hurumin sauraron karar, don haka ya umarci Dansanda mai kara, Inspekta Emmanuel Abdullahi ya mika karar zuwa ofishin babban lauyan jihar.
Daga nan ta dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Janairu na sabuwar shekarar 2018.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng