Albashin 'Yan Majalisan Najeriya ya fi na Shugaban kasar Amurka

Albashin 'Yan Majalisan Najeriya ya fi na Shugaban kasar Amurka

- Albashin Sanatocin Najeriya ya fi na Shugabannin Duniya tsoka

- Shugaban wata Kungiya a Kasar ya bayyana wannan a wani taro

- Areoye Oyebola ya koka da yadda Sanatocin su ka ki rage albashin su

Mun samu labari cewa 'Yan Majalisa a Najeriya sun fi Shugaban Kasar Amurka albashi mai tsoka nesa ba kusa ba.

Albashin 'Yan Majalisan Najeriya ya fi na Shugaban kasar Amurka
'Yan Majalisan Najeriya a wani zama a baya

Shugaban wata Kungiya mai ganin an yi gaskiya da gaskiya a Kasar nan Cif Areoye Oyebola ya bayyana cewa irin albashin da 'Yan Majalisar Dattawar kasar nan su ke tashi da shi a kowane wata ya zarce na Shugabannin manyan kasashen Duniya irin su Amurka da Birtaniya.

KU KARANTA: Tinubu ya zayyana yadda za a gyara tattalin arziki

Kungiyar ta koka da yadda Sanatoci da 'Yan Majalisar Tarayya na kasar su ka tubure su na karbar makudan albashi duk wata na sama da Naira Miliyan 10 ban da kuma alawus iri-iri ba tare da la'akari da halin da ake ciki ba a Kasar na mugun talauci da fatara.

Ba dai yau aka fara kira a rage albashi da alawus na Sanatocin Kasar ba amma shiru kake ji. Oyebola dai yace a sauran kasashen Afrika irin su Ghana ba a fama da wannan matsalar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng