An gurfanar da mai saida kaji a gaban kuliya, ashe kajin nasa ungulu ce ya ke gasawa jama'a

An gurfanar da mai saida kaji a gaban kuliya, ashe kajin nasa ungulu ce ya ke gasawa jama'a

- Ja'irin ashe ba kaji yake sayar ma mutane ba, ungulu ce

- Ya kashe wa kansa kasuwa, kuma ya fada hannun hukuma

- Shin in aka cire yaudara, naman ungulun yana da illa?

A jihar Bayelsa, wata Kungiyar Matasa a Yenagoa sun kama wani Mutum me suya, wanda ke saida wa mutane Naman Angulu akan cewa naman kaza ne a boye.

An gurfanar da mai saida kaji a gaban kuliya, ashe kajin nasa ungulu ce ya ke gasawa jama'a
An gurfanar da mai saida kaji a gaban kuliya, ashe kajin nasa ungulu ce ya ke gasawa jama'a

Ko da yake Kungiyar Matasan ta mika wanda ake tuhuma akan yana saida wa mutane naman angulu akan kaza zuwa ga Jami'an 'yansanda, kuma sun kama shi ne a wata babbar Kasuwa inda ake saida nama, (Tombia Market) inji Comrade Bunas Samuel tare da hadin kan 'yan kungiyar.

Wani Mutum mai suna "Mr Godwin" wanda abin ya faru a gabanshi, yace ya lura kungiyar matasan tayi ta kai komo ne cikin kasuwar kafin tayi kamen.

Yace abin mamaki an ga mushan ungulu guda 30 wanda anriga an shiryasu za a saka su acikin tukunya a tafarfasa su, kafin a akai a saidawa mutane.

DUBA WANNAN: Boko Haram sun farwa sansanin 'yan gudun hijira a Banki, sun kar kma sun kwashe yara

Bayan da yazo hannu, ya kare kansa da cewa, yana amfani da matattun dabbobin ne wajan jan hankalin ungulayen kadai. idan suka sauko suka zo hannu, sai yayi amfani da gubar kemikal ya kashe su.

Yace ya dade yana wannan sana'ar, kuma kwastomomin shi mafi yawansu masu suyan kaza ne da kuma mata.

Babu dai illa cin zallar naman ungulu a kimiyyance, muddin an dafa shi yadda ya dace, an kuma zubda kayan cikin, sannan muddin ba'a kuma kashe ta da guba ba, duk kuwa da cewa abincinta mushe ne.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng