'Maman Prem' (Salman Khan) ta Indiyan Maine Pyar Kiya ta rasu
- Maman Indiya na Maine Pyar Kiya ta rasu a Jihar Mumbai ta Indiya
- Ta fito a Maine Pyar Kiya, fim na Indiya da yayi tashe a shekarun 1990s
- Ta dade tana fama da cutar ciwon zuciya
A yanzu haka a kasar Indiya, ana ta makokin babbar Jaruma Uwa mai fitowa a fina-finai na Indiya, wadda ta shahara wajen fitar da takaicin uwa, kawaici, da kunya na mutanen Indiya, al'adu da suka yi kama da na Hausawa, a Najeriya.
An dai san cewa marigayiyar ta jima tana fama da ciwon zuciya. Sunanta na gaskiya dai Rima Lagoo.
!['Maman Prem' (Salman Khan) ta Indiyan Maine Pyar Kiya ta rasu 'Maman Prem' (Salman Khan) ta Indiyan Maine Pyar Kiya ta rasu](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt732bd50l4cn.jpeg?v=1)
Malama Rima Lagoo dai ta fito a fina-finai da dama, kamar su, Hum Aapke Hai Kaun, Maine Pyar Kiya, Kuch Kuch Hota Hai. An dai sanda a yawan fim da jarumi Salman Khan.
Ta fara shirin fim tana shekara 32 a duniya, da fim din Maine Pyar Kiya, fim na farko da ya fito da Salman Khan. Za'a yi makokin tahalikar a koina a duniya, ciki kuwa harda Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng