Baya Ta Haihu: An kwace Kofin Zakarun Afrika a Hannun Senegal An Mikawa Morocco

Baya Ta Haihu: An kwace Kofin Zakarun Afrika a Hannun Senegal An Mikawa Morocco

  • Hukumar kwallon kafar Afrika (CAF) ta yi hukunci game da korafin da kasar Morocco ta shigar a kan wasan karshe na zakarun Afrika na 2025
  • Bayan sauraron korafin, hukumar ta tabbatarwa kasar Morocco mai masaukin baki nasarar lashe gasar saboda wasu dalilai da ta gabatar
  • Idan ba a manta ba dai kasar Senegel ce ta doke Morocco a wasan karshe da aka yi bayan samun ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan wasan kasashen

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta yanke hukuncin bai wa kasar Morocco kofin gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2025.

Hakan na zuwa ne bayan kwamitin daukaka kara ya yanke hukuncin cewa Senegal ta karya doka a wasan karshe, bayan korafin da hukumar kwallon kafar Morocco ta shigar ya samu nasara.

Kara karanta wannan

Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri

'Yan wasan Senegal bayan lashe kofin AFCON
Lokacin da aka ba Senegal kofin AFCON. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta wallafa cewa hukuncin da aka sanar a jiya Talata ya soke wani hukunci da kwamitin ladabtarwa ya yanke a baya, bayan daukaka kara da Morocco ta yi.

AFCON: Dalilin soke nasarar Senegal

Kwamitin daukaka karar na hukumar CAF ya bayyana cewa ya soke nasarar da kasar Senegal ta samu bayan bincike game da korafin Morocco.

An yanke hukuncin ne bisa tanadin Mataki na 84 na dokokin gasar AFCON, inda kwamitin ya soke hukuncin da kwamitin ladabtarwa ya yanke tare da amincewa da korafin Morocco.

Kwamitin ya ce:

“Lura da abin da tawagar Senegal ta aikata, ta karya Mataki na 82 na dokokin AFCON,”

Ya kara da cewa:

“An amince da daukaka karar da Morocco ta shigar.”

Saboda haka, an ayyana Morocco mai masaukin baki a matsayin zakaran AFCON 2025 ta hanyar hukuncin kwamitin daukaka kara, ba wai ta hanyar sakamakon wasan karshe kai tsaye ba.

Kara karanta wannan

Rasha: Amurka ta fara bakin jini a Turai saboda yakin Iran

Sauran matakan da CAF ta dauka

Game da dan wasan Morocco Ismaël Saibari, kwamitin ya tabbatar da cewa ya aikata rashin da’a wanda ya saba da Matakai na 82 da 83(1) na dokokin ladabtarwa na CAF.

Vanguard ta wallafa cewa an yanke masa hukuncin dakatar da shi a wasanni biyu na CAF, sannan aka soke tarar $100,000 da aka kakaba masa a baya.

'Yan wasan Senegal da Morocco
'Yan kwallon Senegal da Morocco na takaddama filin wasan AFCON. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dangane da batun masu mika kwallo ga 'yan wasa, kwamitin ya dora alhakin laifin da suka yi kan hukumar kwallon kafar Morocco, inda ya rage tarar da aka ci ta zuwa $50,000.

Sai dai daukaka karar da ta shafi katsalandan a wajen duba bidiyon VAR ba ta yi nasara ba, aka tabbatar da tarar $100,000 da aka ci hukumar Morocco a kan wannan batu.

Yadda Senegal ta doke Morocco

A wani labarin kun ji cewa a baya, an bayyana Senegal a matsayin wadda ta lashe kofin AFCON bayan ta doke Morocco da ci 1–0 a wasan karshe da aka buga a Rabat.

Kara karanta wannan

Iran ta shiga matsala: Bataliyar sojojin Amurka mai hatsari ta bar Japan zuwa Gabas

Wasan karshe ya samu tarnaki sakamakon wasu abubuwa da suka faru, ciki har da korafe-korafen ‘yan wasan Senegal da masu horas da su.

An samu tarnaki ne bayan wani hukuncin alkalin wasa a kusa da karshen wasan, da kuma takaddama tsakanin ‘yan wasa, jami’ai da masu gudanar da wasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng