Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohon Dan Wasan Super Eagles Ya Bar Duniya
- Tsohon dan wasan tsakiyar fili na Super Eagles ya rasu yana da shekaru 62 bayan kwashe kwanaki biyar yana jinya a asibiti
- Tsohon abokin wasansa Segun Odegbami ne ya sanar da rasuwarsa, yana cewa Henry Nwosu ya rasu da karfe 4:00 na safiya
- Marigayin ya yi fice a tawagar Green Eagles da ta lashe gasar AFCON na shekarar 1980, kafin daga baya ya zama koci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An shiga jimami bayan sanar da rasuwar tsohon dan wasan kwallon kafa ta Super Eagles a Najeriya.
An sanar da rasuwar Henry Nwosu ne a safiyar ranar Asabar 14 ga watan Maris din shekarar 2026 da muke ciki.

Source: Facebook
An yi rashin tsohon dan wasan Super Eagles
Rahoton Punch ta samu labarin ne ta hannun tsohon abokin wasansa kuma gwarzon gasar AFCON na 1980, Segun Odegbami.
Odegbami ya bayyana cewa Nwosu ya rasu bayan kwanaki biyar yana kwance a asibiti yana fama da rashin lafiya.
Ya ce marigayin ya rasu da misalin karfe 4:00 na safiyar ranar Asabar a asibitin koyarwa na Jami'ar Lagos da ke Ikeja a Lagos.
Odegbami ya ce tun daga ranar Laraba 11 ga watan Maris din shekarar 2026 aka kwantar da shi a sashen kulawa ta musamman yayin da likitoci ke kokarin ceton rayuwarsa.
Ya bayyana rasuwar Nwosu a matsayin babban rashi, yana mai cewa zuciyarsa cike take da bakin ciki yayin sanar da mutuwarsa.

Source: Getty Images
Gudunmawar da Nwosu ya ba Najeriya a kwallo
An haifi Nwosu a Imo, kuma ya kasance daya daga cikin ‘yan wasa mafiya kankanta a tawagar 'Green Eagles' da ta lashe kofin gasar AFCON na shekarar 1980.
Nasarar ta kasance karo na farko da Najeriya ta lashe kofin nahiyar Afirka a gida, cewar The Nation.
An san Nwosu da hazaka wajen taka leda, hangen nesa a filin wasa da kuma kwarewa ta musamman a tsakiyar fili.
Bayan ya yi ritaya daga taka kwallo, marigayin ya ci gaba da hidima ga wasan kwallon kafa ta hanyar zama koci da kuma jagoran matasan ‘yan wasa.
Ya taimaka wajen horar da sababbin ‘yan wasa da dama a harkar kwallon kafa ta Najeriya.
Rasuwarsa ta zo ne kwanaki kadan bayan mutuwar tsohon kocin Super Eagles, Adegboye Onigbinde.
Onigbinde, wanda ya jagoranci Najeriya a gasar cin kofin duniya a shekarar 2002 da aka yi a Japan da South Korea, ya rasu a ranar 9 ga Maris yana da shekaru 88.
Dukkaninsu sun taka muhimmiyar rawa a tarihin tawagar 'Green Eagles' a shekarun 1980.
An yi rashin dan wasan Kannywood a Kano
Kun ji cewa rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani dan wasan kwaikwayo a masana'antar Kannuwood da ake kira Umar Ascon.
Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a asibitin Malam Aminu Kano bayan ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya kafin mutuwarsa.
Marigayin wanda mutane da dama suka fi sani da Alhaji Lado Mai Barkono a shirin Garwashi ya sha ruwan addu'o'i daga al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

