AFCON: Lokuta 8 da Najeriya Ta Zamo Ta 3 a Gasar Zakarun Afrika
Kungiyar kwallon kafan Najeriya ta Super Eagles ta zamo ta uku a gasar zakarun Afrika (AFCON) a lokuta takwas a wasanni daban-daban da ta yi.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwallon ƙafan Najeriya, Super Eagles, na da tarihi na musamman a gasar kofin zakarun Afirka (AFCON).
Duk da cewa ta lashe kofin sau uku, Nijeriya ta fi kowace ƙasa yawan karewa a matsayi na uku, abin da ya sa ake kallonta a matsayin ƙasa mafi yawan lashe tagulla a tarihin gasar.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, mun kawo muku jerin shekarun da Super Eagles ta zamo ta uku a gasar AFCON, ciki har da gasar da aka yi a Morocco a 2025/2026.
1. Najeriya ta fara zama ta 3 a 1976

Kara karanta wannan
Tinubu ya aika sako mai dadi ga 'yan wasan Najeriya bayan sun lallasa Masar a gasar AFCON
Shafin Olumpics ya wallafa cewa Najeriya ta fara zama ta uku a gasar AFCON ta shekarar 1976 da aka gudanar a Habasha, duk da cewa tsarin gasar bai tanadi wasan neman matsayi na uku ba kai tsaye.
An buga zagayen ƙarshe ne ta hanyar rukuni. Najeriya ta kammala gasar a matsayi na uku a teburin rukuni, lamarin da ya zama karon farko da ta samu matsayi na uku a gasar AFCON.

Source: Getty Images
2. Karo na 2 Najeriya ta zamo ta 3
Shekara biyu bayan gasar Habasha, Nijeriya ta sake nuna bajinta a gasar AFCON ta 1978 a da aka gudanar a kasar Ghana da ke Yammacin Afrika.
Rahoton Daily Nation ya nuna cewa bayan rashin kaiwa wasan ƙarshe, kungiyar Super Eagles ta fafata a wasan neman matsayi na uku inda ta samu nasara.
3. Super Eagles ta zo ta 3 a AFCON
Kungiyar harkokin kwallon Afrika ta wallafa cewa bayan shekaru masu yawa ba tare da samun lambar yabo ba, Nijeriya ta dawo da karfinta sosai a gasar a AFCON da aka yi a 2002 a Mali.
Najeriya ta doke ƙasa mai masaukin baki a wasan neman matsayi na uku, ta kuma lashe tagulla. Wannan nasara ta nuna dawowar ƙungiyar cikin manyan ƙasashen Afirka a lokacin.

Kara karanta wannan
AFCON 2025: Gwamnatin tarayya ta tuna da Super Eagles bayan rashin nasara a hannun Morocco

Source: Getty Images
4. Najeriya ta sake zama ta 3 a 2004
The Nation ta rahoto cewa a gasar AFCON ta 2004 da aka yi a Tunisiya, Nijeriya ta fafata a wasan neman matsayi na uku da ya ƙare babu babu zura kwallo.
Wasan ya kare ta bugun fenariti, inda Super Eagles ta yi nasara. Wannan ya zama karo na biyu a jere da Najeriya ke karewa a matsayi na uku a AFCON.

Source: Getty Images
5. A 2006 Najeriya ta sake zama ta 3
Rahoton BDNews24 ya nuna cewa a gasar AFCON ta 2006 da aka yi a kasar Masar, Najeriya ta sake nuna ƙarfinta a nahiyar Afrika.
Bayan faduwa a wasan kusa da na ƙarshe, Super Eagles ta doke Senegal a wasan neman matsayi na uku. Wannan sakamako ya ƙara yawan lokutan da Najeriya ke karewa ta uku.

Source: Getty Images
6. Najeriya ta zama ta 3 a 2010
Gasar AFCON ta 2010 a Angola ta zo da ƙalubale ga Najeriya musamman yadda ta so zuwa wasan karshe amma bata samu zuwa ba.

Kara karanta wannan
Bayan Morocco ta doke Najeriya, BUA ya yi magana kan alkawarin Dalolin kudi da ya yi
Duk da haka, Soccernet ta wallafa cewa ƙungiyar ta sake tattara ƙarfinta, ta doke Algeria a wasan neman matsayi na uku, ta kuma lashe tagulla.

Source: Getty Images
7. Najeriya ta zama ta 3 a 2019 a Masar
A gasar AFCON da aka gudanar a shekarar 2019 a kasar Masar, Nijeriya ta sake nuna bajinta duk da cewa bata kai ga wasam karshe ba.
Bayan faduwa a wasan kusa da na ƙarshe, Africa Soccer ta ce Super Eagles ta doke Tunisia a wasan neman matsayi na uku.

Source: Getty Images
8. Najeriya ta zo ta 3 a kasar Morocco
A gasar AFCON ta 2025/2026 da aka gudanar a Marocco, Nijeriya ta fafata da Masar a wasan neman matsayi na uku bayan gaza zuwa wasan karshe.

Source: Getty Images
Bayan wasan ya ƙare babu ci, BBC ta wallafa cewa an karasa shi ta bugun fenariti inda Nijeriya ta yi nasarar doke kasar Masar da ci 4-2.
Bola Tinubu ya yaba wa Super Eagles
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa 'yan wasan Super Eagles na kasar nan.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba musu ne bayan sun kayar da kasar Masar a bugun fenariti, suka zo na uku a gasar AFCON ta 2025/2026.
'Yan Najeriya ta dama, ciki har da shugabanni da sauran al'umma sun yabawa 'yan kwallon kasar bisa yadda suka yi kokari a gasar.
Asali: Legit.ng
