Tinubu Ya Aika Sako Mai Dadi ga 'Yan Wasan Najeriya bayan Sun Lallasa Masar a Gasar AFCON
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi murna da nasarar da Najeriya ta samu a wasan neman na uku a gasar cin kofin AFCON 2025
- Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta samu galaba kan kasar Masar a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan tashi wasan babu ci
- Tinubu ya ce duk da kashin da Super Eagles ta sha a wasan kusa na karhe, hakan bai hana Najeriya lashe kyautar tagulla ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar Super Eagles murnar nasarar da suka samu a wasan neman na uku a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) 2025.
Shugaba Tinubu ya taya tawagar yan wasan Najeriya murnar lashe lambar tagulla a gasar cin kofin AFCON ta shekarar 2025, wanda ake bugawa a kasar Morocco.

Source: Getty Images
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X a ranar Asabar, 17 ga watan Disamban 2026.
Najeriya ta lallasa kasar Masar
Tawagar Super Eagles ta samu nasara kan takwararta ta kasar Masar a wasan da suka buga a ranar Asabar domin neman na uku a gasar AFCON 2025.
Tawagar ta 'yan wasan Najeriya ta yi nasara ne bayan an yi bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan an tashi wasa babu ci.
Nasarar Super Eagles ta sanya ta samu kyautar tagulla a gasar AFCON 2025 da ke gudana a kasar Morocco, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Bola Tinubu ya jinjinawa Super Eagles
Tinubu ya yabawa Super Eagles bisa yadda suka yi watsi da baƙin cikin shan kashin da suka yi a wasan kusa da na karshe a hannun mai masaukin baki, Morocco, a ranar Larabar da ta gabata.

Kara karanta wannan
AFCON 2025: Gwamnatin tarayya ta tuna da Super Eagles bayan rashin nasara a hannun Morocco
Super Eagles sun yi galaba a kan Masar, wadda ta taɓa lashe AFCON sau bakwai, inda suka doke ta a bugun fenariti bayan karewar lokacin wasa, wasan da ’yan Najeriya suka fi rinjaye a cikinsa.
Shugaba Tinubu ya ce ’yan wasan Super Eagles, ta hanyar wannan nasara, sun sake nuna kudurinsu, jajircewa da zuciyar “za mu iya” da ake dangantawa da Najeriya.
Sakon da Tinubu ya aikawa Super Eagles
"Duk da kyakkyawan kwazon da Eagles suka nuna a gasar, sun sha kashi a wasan kusa da na karshe da Morocco ta hanyar bugun fenariti a ranar Larabar da ta gabata, lamarin da ya karya fatan ’yan kasarmu na lashe kofin."
“Amma ’yan wasanmu ba su yi kasa a gwiwa ba, sun nuna juriyar zuciyar ɗan Najeriya, kokarinsu ya haifar da 'da mai ido."
“Dukkanmu za mu yi alfahari da su yayin da za su karɓi lambar tagulla da suka cancanta a ranar Lahadi a birnin Rabat, Morocco."
“Na gode muku, jaruman Super Eagles. Na gode muku, ’yan wasan tawagar kasarmu. Wannan lambar tagulla tabbas tana da daɗi kamar zinariya.”
- Bayo Onanuga.

Source: Twitter
Gwamnatin Najeriya ta yabi Super Eagles

Kara karanta wannan
Bayan Morocco ta doke Najeriya, BUA ya yi magana kan alkawarin Dalolin kudi da ya yi
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yaba wa tawagar Super Eagles bisa jarumtarsu da ƙwazon da suka nuna a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON).
Gwamnatin ta yi yabon ne duk da rashin nasarar da suka yi a wasan kusa da na karshe da suka kara da tawagar Atlas Lions ta kasar Morocco.
Ta kara da cewa jajircewar tawagar tun daga farko har ƙarshe ta kasance abin alfahari ga kasar, duk kuwa da irin sakamakon da aka samu.
Asali: Legit.ng
