AFCON 2025: Osimhen Ya Fadi Yadda Super Eagles Ke Kallon Wasa da Morocco
- 'Dan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, ya yi tsokaci kan wasan da Supers Eagles za ta yi da takwararta ta kasar Morocco
- Victor Osimhen ya nuna cewa 'yan wasan Super Eagles sun fi maida hankali a koda yaushe kan abin da ke gabansu
- 'Dan wasan ya bayyana cewa sun riga sun nunawa duniya cewa ba da wasa suka zo ba a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Rabat, Morocco - Dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ya yi magana kan wasan da Najeriya za ta yi da kasar Morocco.
Victor Osimhen ya ce babu wata matsin lamba a kan tawagar Najeriya gabanin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) da za su fafata da Morocco.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana gabanin wasan a wata hira da tashar CBSSportsGolazo.

Kara karanta wannan
AFCON 2025: Gwamnatin tarayya ta aika sako ga Super Eagles yayin da take shirin fafatawa da Morocco
Najeriya za ta fafata da Morocco a AFCON
Najeriya za ta kara da Morocco ne ranar Laraba, 14 ga watan Janairun 2026 da misalin ƙarfe 9:00 na dare agogon Najeriya, domin neman tikitin zuwa wasan karshe na AFCON 2025.
Morocco ce ke karɓar bakuncin gasar, kuma za a buga wasan a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat, babban birnin ƙasar, wanda ke da kujeru kusan 70,000.
Ana sa ran magoya bayan ƙasar Morocco za su mamaye filin wasa a wannan karawar.
Me Victor Osimhen ya ce kan wasan?
Osimhen ya amince cewa Morocco na da fa’idar buga wasa a gida, amma ya ce ’yan wasan Super Eagles da dama sun saba da buga wasa a manyan filayen da ke da cunkoso fiye da haka, kuma sun yi fice a irin waɗannan yanayi masu tsoratarwa.
Ya ƙara da cewa duk da cewa Morocco na da “tawaga mai karfi”, Najeriya ta riga ta gina suna a gasar a matsayin “ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da aka fi jin tsoro”.
“Idan aka yi la’akari da irin 'yan wasan da muke da su a cikin tawagar, ina ganin babu wani matsin lamba a sansaninmu. Ba mu tattauna batun tawagar Morocco a sansanin; muna ɗaukar wasa ɗaya bayan ɗaya ne kawai."
“Mun dai fafata da babbar kasa kamar Algeria, kuma mun nuna abin da duniya baki ɗaya ta gani cewa waɗannan ’yan wasan na da cikakken shiri domin lashe kofin.”
“Amma tabbas ba zai zama wasa mai sauƙi ba, domin 'yan Morocco za su buga a gaban dubban magoya bayansu, wanda hakan fa’ida ce a gare su.”
“Ina ganin da dama daga cikinmu a Super Eagles mun buga wasa a filayen da ke ɗaukar mutum 80,000 ko 90,000.”
“Don haka a gare ni kai tsaye, babu wani matsin lamba ko kaɗan. Ina mai da hankali ne kawai kan tawagata, kuma idan ranar wasa ta zo, za mu ba da dukkan kokarinmu muna fatan samun nasara. Ba zai zama da sauƙi ba, amma ina ganin muna da dama.”
- Victor Osimhen

Source: Twitter
Osimhen na taka rawar gani a AFCON 2025
Osimhen ya zura kwallaye huɗu a gasar zuwa yanzu, kuma yana cikin manyan ’yan wasan da suka fi cin kwallaye.
Haka kuma, kwallaye biyu ne kawai suka rage masa ya kai tarihin matsayin wanda ya fi cin kwallaye a Super Eagles da marigayi Rashidi Yekini ya kafa.
Gwamnatin Najeriya ta karfafi Super Eagles
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta karfafa gwiwar 'yan wasan Super Eagles kan wasan da za su yi da Morocco.
Gwamnatin tarayya ta bukaci 'yan wasan Super Eagles da su buga wasan cikin kwarin gwiwa da haɗin kai a fafatawar da za su yi da Morocco a zagayen na kusa da na karshe.
Ta bayyana cewa tawagar ta nuna zuwa yanzu ta sake tunatar da ’yan Najeriya dalilin da ya sa Super Eagles ke ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin kungiyoyin da aka fi girmamawa a nahiyar Afrika.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

