AFCON 2025: Mourinho Ya Hango Kasar da Za Ta Yi Nasara a Wasan Najeriya da Moroko
- Jose Mourinho ya yi hasashen kasar da za ta yi nasara a wasan kusa da karshe na gasar AFCON 2025 tsakanin Najeriya da Morocco
- Tsohon kocin Manchester United ya kafa hujjoji na dalilin da ya sa yake ganin kasar da ya zaba za ta tsallaka zuwa wasan karshe
- Yanzu haka da dan wasan Morocco Brahim Diaz ne ke gaba zura kwallaye da ci biyar yayin da Victor Osimhen ke da kwallaye hudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Morocco - Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Benfica, Jose Mourinho, ya bayyana ra’ayinsa game da fafatawar da za a yi a daren yau tsakanin Super Eagles da Atlas Lions.
Najeriya da Morocco (mai masaukin baki) za su fafata ne a wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika na shekarar 2025.

Kara karanta wannan
AFCON 2025: Gwamnatin tarayya ta aika sako ga Super Eagles yayin da take shirin fafatawa da Morocco

Source: Getty Images
Haduwar Najeriya da Morocco a AFCON 2025
Mourinho, wanda tsohon kocin Manchester United da Chelsea ne, ya bayyana Morocco a matsayin ƙasa mafi ƙarfi da kowa ya kamata ya ji tsoronta a nahiyar Afirka a halin yanzu, in ji rahoton Own Goal Nigeria.
Najeriya ta kai wannan mataki ne bayan nuna bajinta da tumurmusa Algeria da ci 2-0 a wasan daf da na kusa da na ƙarshe, inda Victor Osimhen da Akor Adams suka zura ƙwallayen.
A hannu guda kuma, Morocco ta samu tikitin wannan mataki ne bayan ta doke zakarun nahiyar sau biyar, wato Kamaru, da ci 2-0, ta hanyar ƙwallayen da tauraron Real Madrid, Brahim Diaz, da Ismail Saibari suka zura.
Najeriya ta zura ƙwallaye 14 a gasar zuwa yanzu, yayin da Morocco ta zura guda tara amma ba a cika zura mata ƙwallo ba, a cewar wani rahoto na BBC.
Mourinho ya fadi kasar da za ta yi nasara
Mourinho, mai shekaru 62, wanda ake yi wa laƙabi da "The Special One", ya bayyana cewa tsari, tarbiyyar ’yan wasa, da kuma kwarin gwiwa su ne za su ba wa Morocco nasara a kan Najeriya a wasan da za a fafata a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat.
Mourinho ya bayyana cewa:
“Morocco ita ce ƙungiya ta ɗaya a Afirka kuma su ne za su lashe AFCON 2025. Ƙungiya ce mai tsari da tarbiyya wadda ta yi imanin za ta iya yin nasara a kowane yanayi.
"Sun riga sun nuna cewa su ba ’yan kallo ba ne a fagen duniya lokacin da suka zo na huɗu a gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar.”

Source: Twitter
Burin kafa tarihi a birnin Rabat
Kocin Morocco, Walid Regragui, ya amince da cewa wasan zai kasance mai cike da ƙalubale, amma ya jaddada cewa tun shekarar 2004 ƙasarsa ba ta kai ga matakin kusa da na ƙarshe ba, don haka a wannan karon burinsu shi ne su kafa sabon tarihi a gida.
Ya bayyana cewa kodayake suna girmama Super Eagles, amma ’yan wasansa sun shirya tsaf don kai wa ga wasan ƙarshe, in ji rahoton The Nation.
Fafatawar yau 14 ga watan Janairu, 2026, za ta raba gardama tsakanin manyan ’yan wasan gaba na nahiyar, inda Brahim Diaz ke jagorantar masu zura ƙwallaye da guda biyar, yayin da Victor Osimhen ke biye da shi da ƙwallaye hudu.
Morocco ta gamu da matsala a AFCON 2025
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kocin Morocco, Walid Regragui, ya tabbatar da cewa babban ɗan wasan tsakiyarsu, Azzedine Ounahi, ba zai buga wasa da Najeriya ba.
Walid Regragui ya ce Ounahi ba zai samu damar buga wasan kusa da na ƙarshe na gasar AFCON 2025 da za su fafata da Super Eagles ta Najeriya a yau Laraba, 14 ga Janairu, 2026.
Wannan sanarwa ta zo ne a matsayin babban kalubale ga kasar mai masaukin baki, duba da irin muhimmancin da dan wasan yake da shi a tsarin wasan Regragui.
Asali: Legit.ng

