AFCON 2025: Morocco Ta Gamu da Babbar Matsala Tana Shirin Karawa da Najeriya
- Kocin Morocco Walid Regragui ya tabbatar da cewa dan wasa Azzedine Ounahi ba zai buga wasan Najeriya ba saboda raunin da samu
- Super Eagles zata rasa Wilfred Ndidi sakamakon katin gargadi biyu yayin da kocin Luc Eymael ke hasashen Morocco za ta lallasa Najeriya
- Najeriya da Morocco za su fafata a daren yau a birnin Rabat domin neman gurbin shiga wasan karshe na gasar AFCON ta shekarar 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Morocco - Kocin tawagar Atlas Lions ta Morocco, Walid Regragui, ya tabbatar da cewa za su rasa babban ɗan wasan tsakiyarsu, Azzedine Ounahi, a wasansu da Najeriya
Walid Regragui ya ce Ounahi ba zai samu damar buga wasan kusa da na ƙarshe na gasar AFCON 2025 da za su fafata da Super Eagles ta Najeriya a yau Laraba, 14 ga Janairu, 2026.

Source: Getty Images
Morocco ta samu matsala gabanin wasa da Najeriya
Wannan sanarwa ta zo ne a matsayin babban kalubale ga kasar mai masaukin baki, duba da irin muhimmancin da dan wasan yake da shi a tsarin wasan Regragui, in ji rahoton Own Goal Nigeria.
Ounahi, ɗan shekara 25, bai riga ya warke daga raunin da ya sanya ya rasa wasannin zagaye na 16 da na kusa da na kusa da na ƙarshe ba.
Rabon sa da buga wasa tun nasarar da suka samu a kan Zambia da ci 3-0 a matakin rukuni, inda ya taimaka aka zura ƙwallaye biyu.
Ko da yake Regragui ya yi wa manema labarai wasan barkwanci da farko cewa ɗan wasan ya dawo, daga baya ya tabbatar da cewa:
“Ina maku wasa ne, Ounahi ba zai buga wasan ba saboda rauni. Sai dai Kyaftin Romain Saïss ya warke kuma zai iya taka leda.”
Nakasu ga Najeriya a karawa da Morocco
A hannu guda, Najeriya ma za ta fuskanci nakasu a tsakiyar fili, domin Kyaftin Wilfred Ndidi ba zai buga wasan ba saboda dakatarwa bayan ya samu katin gargadi biyu a wasannin baya.
Legit Hausa ta rahoto cewa wannan zai tilasta wa kocin Super Eagles neman wanda zai maye gurbin Ndidi domin fuskantar barazanar Morocco a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat.
Tsohon kocin Chippa United, Luc Eymael, ya yi hasashen cewa Morocco ce za ta yi nasara a kan Najeriya, in ji rahoton Flash Score.

Source: Instagram
'Morocco ce za ta ci wasan' - Eymael
Eymael ya bayyana cewa Morocco tana buga ƙwallo a tsari mai kyau kuma za ta samu tarin magoya baya da suka kai 70,000 a filin wasanta na gida.
Ya tunatar da cewa Najeriya na da tarihin rashin nasara kwanan nan, ciki har da rasa gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 a hannun DR Congo.
A cewarsa, ko da yake duka ƙasashen biyu za su ci ƙwallo, amma Morocco ce za ta kai wasan ƙarshe na AFCON 2025.
Wannan fafatawa ta yau 14 ga Janairu, 2026, ita ce ta shida tsakanin ƙasashen biyu a tarihin AFCON, kuma ita ce ta farko cikin shekaru 22.
'Najeriya za ta lallasa Morocco' - Bature
A wani labarin na daban, Legit Hausa ta rahoto cewa wani bature ya yi hasashen cewa Najeriya ce za ta lallasa Morocco a wasan kusa da na karshe na gasar AFCON 2025.
Baturen wanda ya yi amfani da kwan roba wajen samar da hasashensa, ya nuna cewa Morocco za ta sha kashi a hannun Super Eagles, ko da kuwa za ta zura kwallaye.
Masu sharhi sun yi gargadin cewa rashin nasarar Najeriya na iya haifar da zargin nuna son kai ga kasar Morocco dake masaukin bakin gasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


