AFCON 2025: An Fadawa Najeriya abin da Za Ta Yi don Doke Morocco a 'Semi Finals'
- Odion Ighalo ya bukaci Super Eagles su kasance masu karfin zuciya domin doke Morocco da za ta samu goyon bayan mutane 70,000 a Rabat
- Najeriya dake da kwallaye 14 a gasar AFCON 2025 za ta fafata da Morocco a ranar Laraba domin neman gurbin shiga wasan karshe
- Tsohon ɗan wasan gaba na Man United da Super Eagles, Odion Ighalo, ya kawo dabarun da Najeriya za ta yi amfani da su a wasan yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon ɗan wasan gaba na Manchester United da Super Eagles, Odion Ighalo, ya gargaɗi Najeriya yayin da take shirin karawa da Morocco a ranar Laraba, 14 ga Janairu, 2026.
Odion Ighalo ya ce dole ne 'yan wasan Super Eagles su ƙara kaimi da kashi 100 idan har suna son ruguza mafarkin Morocco na lashe kofin AFCON 2025 a gida.

Source: Getty Images
An gargadi Najeriya kan karfin Morocco
Ighalo, wanda shi ne ya lashe takalmin zinare a AFCON 2019, ya bayyana dabarun da Najeriya za ta iya amfani da su ne a sharhin wasanni da ya yi a tashar SuperSport, in ji rahoton Soccernet.
Tsohon ɗan wasan gaba na Manchester United ya bayyana cewa wasan da Najeriya ta doke Algeria a matakin kusa da na ƙarshe ba zai isa ya doke Morocco ba.
A cewarsa, matasan 'yan wasan Morocco suna da sauri, fasaha, da kuma kwarin gwiwa, musamman duba da cewa kusan duka 'yan wasan ne suka kafa tarihin kai wa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar.
"Dole yan wasa su kara karfin zuciya" - Ighalo
Ighalo ya jaddada cewa babban ƙalubalen da Super Eagles za su fuskanta shi ne matsin lamba daga kusan magoya baya 70,000 da za su cika filin wasa na Prince Moulay Abdellah.

Kara karanta wannan
Shehu Sani ya magantu bayan Amurka ta kawo tallafin kayan aiki ga sojojin Najeriya
"Dole ne 'yan wasan su kasance a shirye ta fuskar tunani. Za su fuskanci babban matsin lamba...
"Idan Najeriya tana son yin nasara, dole ne su yi ƙoƙari fiye da yadda suka yi da Algeria sannan su toshe kunne daga abubuwan da za su ji a wannan filin wasan. Na yi imanin suna da damar yin hakan."
- Odion Ighalo.

Source: Getty Images
Tarihin haɗuwar Najeriya da Morocco
Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 22 da ƙasashen biyu za su haɗu a gasar AFCON. Rabon da su haɗu tun a shekarar 2004 inda Morocco ta doke Najeriya da ci 1-0.
A tarihin AFCON, ƙasashen biyu sun haɗu sau biyar, inda Morocco ta yi nasara sau uku, Najeriya kuma sau biyu.
Duk da cewa an fi ganin Morocco ce za ta yi nasara, ita ma Najeriya tana taƙama da nasararta a duka wasanninta biyar na wannan gasar, inda ta zura ƙwallaye 14—mafi yawa a gasar zuwa yanzu.
Bature ya yi hasashen nasarar Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani Bature ya yi hasashen yadda za ta kaya a wasan kusa da na karshe na gasar AFCON a ranar Laraba, 14 ga Janairu, 2025.
Baturen ya yi amfani da ƙwai guda biyu (wadanda ya sanya wa launukan koraye da ja) domin yin hasashen sakamakon wasan tsakanin Najeriya da Morocco.
An ga yadda jar kwallo, wacce ke alamta Morocco ta shiga rami sau uku, kafin koriyar kwallo, wacce ke alamta Najeriya ta zo ta shiga ramin har sau hudu, wanda ya nuna Najeriya ce za ta ci wasan.
Asali: Legit.ng

