Bayan Korar Ruben Amorim, An Nada Sabon Kocin Kungiyar Manchester United

Bayan Korar Ruben Amorim, An Nada Sabon Kocin Kungiyar Manchester United

  • Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta cimma yarjejeniyar nada tsohon 'dan wasanta, Michael Carrick a matsayin sabon koci na wucin gadi
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an gama rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta ba Carrick damar jagorantar Man United zuwa karshen kakar bana
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kungiyar ta sallami tsohon kocinta, Ruben Amorim daga aiki bayan ya soki shugabannin Man United

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Manchester, UK - Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta nada sabon mai horarwa, wanda zai jagoranci babbar tawagar 'yan wasanta zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Man United na dab da sanar da nadin tsohon dan wasan tsakiyar kungiyar, Michael Carrick, a matsayin sabon koci na wucin gadi.

Kara karanta wannan

Neman sulhu: Ƴan bindiga sun gindaya wa gwamnatin Katsina sharudda 8 masu tsauri

Michael Carrick.
Sabon mai horar da Manchester United na wucin gadi, Michael Carrick Hoto: Michael Carrick
Source: Facebook

Man United ta kulla yarjejeniya da Carrick

Fitaccen mai kawo labaran cinikin 'yan wasa, Fabrizio Romano, ne ya tabbatar da wannan labari a shafinsa na Facebook a yau Talata, 13 ga watan Janairu, 2025.

Romano ya bayyana cewa an kulla yarjejeniya tsakanin Man United da Carrick tun jiya Litinin, 12 ga watan Janairu, 2025.

Ya kara da cewa a yanzu an kammala kowane sashe na yarjejeniyar kuma kowane bangare ya rattaba hannu, har ma da batun ma'aikatan da za su taimaka wa Carrick a aikinsa.

Carrick ya rattaba hannu a Man United

A sakon da ya wallafa, Romano ya ce:

"Michael Carrick ya sanya hannu a matsayin sabon kocin Manchester United na wucin gadi har zuwa karshen kakar wasa.
"An cimma yarjejeniyar baka tun jiya, kuma yanzu an kammala komai ciki har da tawagar mai horarwa. Ana sa ran sanarwa daga kungiyar nan ba da jimawa ba."

Kara karanta wannan

'Dole a sake shi,' Atiku ya harzuka da aka garkame matashin da ke sukar Tinubu

Carrick, wanda tsohon dan wasan kungiyar Man United ne kuma tsohon koci a karkashin tsofaffin masu horarwa, ya dawo a wani muhimmin lokaci.

A lokacin da Carrick ya jagoranci Man United a wasanni uku kafin nada sabon koci a 2021, ya samu nasara a wasanni biyu, Villarreal da Arsenal, sannan ya yi kunnen doki da Chelsea, cewar rahoton ESPN.

Michael Carrick.
Tsohon dan wasan tsakiya na Manchester United, Michael Carrick Hoto: Michael Carrick
Source: Facebook

Abubakar Nakowa, wani mai goyon bayan Man United a jihar Katsina ya shaidawa Legit Hausa cewa suna maraba da wannan sauyi da kulob din ya yi.

Ya tuna lokacin da Carrick ya jagoranci yan wasan Man United bayan korar Ole Gunnar Solskjaer a shekarar 2021, inda kocin ya lallasa Arsenal da Villarreal a wasanni uku da ya jagoranta.

"Muna son Carrick, ko lokacin da aka ba shi rikon kwarya a 2021, na so a nada shi koci na dindindin, saboda na ji dadin wasan da ya jagoranci Man U ta lallasa Arsenal."
"Muna masa fatan alheri, domin zai karbi aiki a lokaci mai wahala, wanda kungiyarmu ke bukatar nasara, burinmu mu fito gasar nahiyar Turai a kaka mai zuwa," in ji shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kashe Naira biliyan 40 a zamanantar da gadar Legas da CCTV

Dalilan korar kocin Man United

A baya, mun kawo muku cewa Manchester United ta raba gari da mai horar da manyan 'yan wasanta, Ruben Amorim bayan ya shafe watanni 14 a kulob din.

Man United, wacce ke fafatawa a gasar cin kofin Firimiya na kasar Ingila ta mika godiyarta ga Amorim bisa gudummuwar da ya bayar a tsawon lokacin da ya shafe yana aiki.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin da ya taso kwa nan nan tsakanin kulob din da kocin ne ya janyo tangarda a dangantakarsu, lamarin da ya kai ga korar Amorim daga aikinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262