AFCON 2025: Bature Ya Hango Kasar da Za Ta Yi Nasara a Wasan Najeriya da Morocco
- Wani bature ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ya yi amfani da ƙwai wajen hasashen cewa Najeriya zata doke Morocco a gasar AFCON 2025
- Ma'abota yanar gizo sun bayyana ra'ayoyi daban-daban inda wasu suka ce Najeriya zata samu nasara idan aka yi adalci a wasan na gobe
- Masu sharhi sun yi gargadin cewa rashin nasarar Najeriya na iya haifar da zargin nuna son kai ga kasar Morocco dake masaukin bakin gasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda wani Bature ya yi hasashen yadda za ta kaya a wasan kusa da na karshe na gasar AFCON a gobe Laraba.
Baturen ya yi amfani da ƙwai guda biyu (wadanda ya sanya wa launukan koraye da ja) domin yin hasashen sakamakon wasan tsakanin Najeriya da Morocco.

Source: Twitter
Hasashen wasan Najeriya da Morocco
A cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa ta TikTok, mutumin ya zubar da ƙwan guda biyu lokaci ɗaya domin ganin wanda zai yi nasara.
An ga yadda jar kwallo, wacce ke alamta Morocco ta shiga rami sau uku, kafin koriyar kwallo, wacce ke alamta Najeriya ta zo ta shiga ramin har sau hudu, wanda ya nuna Najeriya ce za ta ci wasan.
Wannan hasashen ya janyo ce-ce-ku-ce daga ’yan Najeriya a ƙarƙashin bidiyon, inda wasu suka yi masa gargaɗin cewa ya gode wa Allah da ya nuna Najeriya ce za ta ci, idan ba haka ba da ya fuskanci fushin dubban masu amfani da yanar gizo.
Wasu kuwa sun yi imanin cewa wannan wasa da za a yi ranar Laraba, 14 ga Janairu, 2026, zai kasance mai zafi sosai duba da yadda Morocco ce mai masaukin baƙi.
Nasarar Najeriya da Moroko a wasannin baya
Wasan kusa da na ƙarshen tsakanin Super Eagles da Atlas Lions zai gudana ne a babban filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke birnin Rabat.
Najeriya ta isa wannan mataki ne bayan ta doke Algeria da ci 2-0 a wasan daf da na kusa da na ƙarshe, inda Victor Osimhen da Akor Adams suka zura ƙwallayen, in ji rahoton Legit Hausa.
A hannu guda kuma, Morocco ta doke Kamaru ne da ci 2-0 don tabbatar da matsayinta, tare da shiga zagayen kusa da na karshe, a cewar rahoton BBC.

Source: Getty Images
Abin da zai faru idan Najeriya ta sha kasa
Wani matashi ɗan Najeriya mai suna Menjo shi ma ya bayyana ra'ayinsa kan wasan, inda ya gargaɗi hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) da alkalan wasa.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Menjo ya ce:
- Idan Najeriya ta doke Morocco, komai zai tafi lafiya lau.
- Amma, idan Morocco ta doke Najeriya, "to lamura za su cukurkude."
Ya bayyana cewa idan Najeriya ta sha kashi, ’yan ƙasar za su zargi CAF da nuna son kai ga Morocco a matsayinta na mai masaukin baki, ko kuma zargin alƙalin wasa da rashin adalci wajen bayar da fanareti ko soke ƙwallaye.

Kara karanta wannan
"Ina ya shiga?" Peter Obi ya fito da damuwarsa game da yawan tafiye tafiyen Tinubu
Najeriya na neman kofinta na hudu ne, yayin da Morocco ke son kafa tarihi a gida tun bayan nasarar su ta karshe a 1976.
BUA ya gwangwaje 'yan wasan Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Abdulsamad Rabiu ya taya Super Eagles murnar doke Algeria, tare da alkawarin ba ’yan wasan kyautar N700,000.
Abdussamad Rabiu ya ce zai ƙara ba da $50,000 kan kowace kwallo da aka ci a wasan kusa da na ƙarshe da Najeriya za ta buga a gasar bana.
Attajirin Najeriyar ya kuma yi alkawarin $1,000,000 idan Super Eagles ta lashe wasan ƙarshe, tare da ƙarin $100,000 ga kowace kwallo da aka ci a Morocco.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

