AFCON2025: Najeriya Ta Gamu da Babban Cikas yayin da Take Shirin Haduwa da Moroko

AFCON2025: Najeriya Ta Gamu da Babban Cikas yayin da Take Shirin Haduwa da Moroko

  • Kyaftin din Super Eagles Wilfred Ndidi ba zai buga wasan kusa da na karshe da Morocco ba sakamakon tara katin gargadi guda biyu
  • Victor Osimhen ya sha alwashin cewa Najeriya za ta lallasa Morocco mai masaukin baki domin kai wa wasan karshe na gasar AFCON 2025
  • Najeriya za ta fafata da Morocco ranar Laraba 14 ga watan Janairu yayin da kocin Eagles ke neman wanda zai maye gurbin Ndidi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Morocco - Labari mara daɗi ya iske masoyan ƙwallon ƙafa a Najeriya yayin da aka tabbatar da cewa kyaftin ɗin Super Eagles kuma babban ɗan wasan tsakiya, Wilfred Ndidi, ba zai buga wasan kusa da na ƙarshe da za su fafata da ƙasar Morocco ba.

Ndidi ya samu dakatarwar wasa ɗaya ne sakamakon tara katin gargadi guda biyu (yellow cards) a lokacin wasannin da suka gabata.

Kara karanta wannan

'Yan wasan Najeriya sun tumurmusa Algeria, sun tsallaka zuwa mataki na gaba a AFCON

Kyaftin din Super Eagles, Ndidi ba zai buga wasan Najeriya da Mokoro ba.
Kyaftin din Super Eagles, Wilfred Ndidi da tawagar 'yan wasan Najeriya a AFCON 2025. Hoto: @NGSuperEagles
Source: UGC

Ndidi ba zai buga wasan Najeriya da Moroko ba

Ndidi ya karɓi katin farko ne a wasan zagaye na 16 da Najeriya ta doke Mozambique, sannan ya sake karɓar wani katin a wasan kusa da na kusa da na ƙarshe da suka doke Algeria da ci 2-0 a ranar Asabar, in ji rahoton Punch.

A wasan na Algeria, an ba Ndidi katin ne a minti na 67 saboda jinkirta wasa, kafin daga bisani a sauya shi a minti na 69 sakamakon raunin jijiyar cinya da ya ji.

Kodayake ba a tantance girman raunin ba, katin gargadin ya riga ya raba shi da wasan Morocco ko da yana da lafiya.

Wanene zai maye gurbin Ndidi?

Rashin Ndidi, wanda ke buga wa ƙungiyar Besiktas wasa, babban gibi ne ga tsakiyar Najeriya duba da irin ƙwarewarsa da jagoranci.

Akwai rahotannin cewa kocin Super Eagles, Eric Chelle, na shirin amfani da Raphael Onyedika na kungiyar kwallon kafar Brugge a matsayin madadin Ndidi.

Kara karanta wannan

AFCON: BUA zai ba Super Eagles $500,000, ya yi masu alkawarin N1bn a wasan ƙarshe

Haka kuma, Frank Onyeka da Calvin Bassey sun tsallake rijiya da baya inda ba su karɓi katin da zai dakatar da su ba a wasan gaba ba, in ji rahoton Pulse Sport Nigeria.

Bisa dokokin gasar AFCON, ana soke dukkan katinan gargadi bayan wasan kusa da na ƙarshe. Wannan yana nufin idan Najeriya ta kai wasan ƙarshe, Ndidi zai samu damar buga wasan.

Ana sa ran fafata wannan gagarumin wasa da "Atlas Lions" na Morocco a ranar Laraba, 14 ga Janairu, 2026, a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat.

Victor Osimhen ya ce Najeriya za ta lallasa Morocco a wasan kusa da karshe na gasar AFCON 2025.
'Yan wasan Super Eagles a filin wasa yayin buga gasar AFCON 2025. Hoto: @NGSuperEagles
Source: Getty Images

"Zamu lallasa Morocco" — Osimhen

Babban ɗan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, ya yi alkawarin cewa Super Eagles za ta ba da mamaki wajen lallasa Morocco mai masaukin baki domin kai wa wasan ƙarshe.

Osimhen, wanda shi ne ya buɗe raga a minti na 47 a wasan da suka doke Algeria, ya bayyana cewa ba sa tsoron kowace ƙungiya, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Osimhen ya shaida wa manema labarai cewa:

“Muna girmama Morocco saboda kwararrun ’yan wasa da suke da su, amma ba mu fargaba. Zamu yi amfani da dukkan ƙarfinmu da jajircewarmu don samun nasara.”

Kara karanta wannan

An yanke wa wani 'dan Najeriya hukuncin kisa a kasar waje, za a rataye shi

Ya ƙara da cewa nasarar da suka samu a kan Algeria ta ƙara musu kwarin gwiwa, kuma za su ci gaba da taka leda da irin wannan kishin ƙasa har zuwa wasan ƙarshe.

BUA zai ba Super Eagles kyautar $600,000

A wani labari, mun ruwaito cewa, attajirin Najeriya, Abdulsamad Rabiu ya taya Super Eagles murnar doke Algeria, tare da alkawarin ba ’yan wasan kyautar $500,000.

Abdussamad Rabiu ya ce zai ƙara ba da $50,000 kan kowace kwallo da aka ci a wasan kusa da na ƙarshe da Najeriya za ta buga a gasar bana.

Ya kuma yi alkawarin $1,000,000 idan Super Eagles ta lashe wasan ƙarshe, tare da ƙarin $100,000 ga kowace kwallo da aka ci a Morocco.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com