'Yan Wasan Najeriya Sun Tumurmusa Algeria, Sun Tsallaka zuwa Mataki na Gaba a AFCON
- Tawagar Super Eagles ta samu nasara kan takwararta ta Algeria da ci 2-0 a wasan daf da na kusa da na karshe da suka kara yau Asabar
- Najeriya ta zura kwallaye biyu a ragar Algeria ne ta hannun zakakurin 'dan wasan gabanta, Victor Osimhen da Akor Adams
- Wannan ya ba Najeriya damar tsallakawa zuwa mataki na gaba, inda za ta gwabza da Morocco mai masaukin baki a wasan kusa da na karshe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Morocco - 'Yan wasan kwallon kafa na Najeriya sun samu nasara a wasan daf da na kusa da na karshe da suka kece raini da Algeria a gasar AFCON 2025.
'Dan wasan gaba na tawagar Super Eagles, Victor Osimhen ya zura kwallo daya tare da taimakawa aka zura wata, yayin da Najeriya ta doke Algeria da ci 2–0.

Kara karanta wannan
AFCON: BUA zai ba Super Eagles $500,000, ya yi masu alkawarin N1bn a wasan ƙarshe

Source: Twitter
Super Eagles ta tsallaka mataki na gaba
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan nasara dai ta kai Super Eagles zuwa wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka watau AFCON 2025.
Gabanin wasan daf da na kusa da na karshe, hankula sun karkata ne kan fadan da Osimhen ya yi da wasu abokin wasansa a wasan zagaye na 16.
Haka zalila an yi ta ce-ce-ku-ce kan batun barazanar da tawagar Super Eagles ta yi sakamakon rashin biyan alawus-alawus.
Yadda Najeriya ta lallasa Algeria a AFCON
Sai dai duk da haka Najeriya ta nuna bajinta, inda ta zura kwallaye biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, sakamakon gudunmawar Osimhen.
Najeriya ta mamaye mintuna 45 na farko baki daya, inda ta kai hare-hare masu hadari gidan Algeria kuma ta hana abokan karawar su kai wa mai tsaron ragarta, Stanley Nwabali hari ko sau daya.
Mai tsaron bayan Najeriya, Calvin Bassey ya kusa zura kwallo amma Ramy Bensebaini ya fitar da kwallon daga layin raga, sannan bayan duba na'urar VAR aka yanke hukuncin cewa ba ta haura layi ba.
A doka dole sai kwallo ta gama tsallaka layi sannan alkali yake hura cewa an zura ta a raga.
Victor Osimhen ya nuna bajinta
Amma mintuna biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Osimhen ya tashi sama ya buga kwallon da kai kuma ya zura kwallo, ya ba Najeriya jagoranci da ta dace.
Wannan ita ce kwallo ta hudu ta dan wasan gaban Najeriya ya zura a gasar AFCON, kuma ta 35 a tarihin wasannin da ya buga wa kasarsa, in ji Vanguard.

Source: Getty Images
Najeriya ta kara ta biyu a minti na 57, lokacin da Iwobi ya tura kwallo ga Osimhen, wanda ba tare da son kai ba ya miƙa wa Adams, shi kuma ya samu damar yanke gola tare da zura kwallon cikin sauki
A halin yanzu dai Najeriya ta kai wasan kusa da na karshe na AFCON karo na 16 a tarihinta, inda za ta kara da kasar Morocco mai masaukin baki domin neman tikitin zuwa wasan karshe.
Shugaban BUA ya yi wa Super Eagles kyauta
A baya, kun ji cewa shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdulsamad Rabiu ya taya Super Eagles murnar doke Algeria, tare da alkawarin ba ’yan wasan kyautar dala $500,000.
Attajirin ya ce zai ba da $100,000 ga kowace kwallon da aka ci a wasan kusa da na karshe da Super Eagles za ta buga da Morocco.
Abdulsamad Rabiu ya kuma bayyana cewa idan har kungiyar ta kai ga wasan karshe kuma ta yi nasara, zai ba da kyautar $1,000,000.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

