AFCON: BUA Zai ba Super Eagles $500,000, Ya Yi Masu Alkawarin N1bn a Wasan Ƙarshe

AFCON: BUA Zai ba Super Eagles $500,000, Ya Yi Masu Alkawarin N1bn a Wasan Ƙarshe

  • Attajirin Najeriya, Abdulsamad Rabiu ya taya Super Eagles murnar doke Algeria, tare da alkawarin ba ’yan wasan kyautar N700,000
  • Abdussamad Rabiu ya ce zai ƙara ba da $50,000 kan kowace kwallo da aka ci a wasan kusa da na ƙarshe da Najeriya za ta buga a gasar bana
  • Ya kuma yi alkawarin $1,000,000 idan Super Eagles ta lashe wasan ƙarshe, tare da ƙarin $100,000 ga kowace kwallo da aka ci a Morocco

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Attajiri a Najeriya, Abdulsamad Rabiu ya taya kungiyar Super Eagles murnar doke Algeria a gasar AFCON da ake yi.

Abdulsamad Rabiu zai kuma ba yan wasan kyautar $1m musamman idan suka yi nasara a wasan karshe wanda ya kai fiye da Naira biliyan daya.

Kara karanta wannan

'Yan wasan Najeriya sun tumurmusa Algeria, sun tsallaka zuwa mataki na gaba a AFCON

Abdulsamad Rabiu zai ba Super Eagles $500,000
Attajiri Abdulsamad Rabiu yana kallon wasan Najeriya. Hoto: Abdul Samad Rabiu, CFR, CON.
Source: Facebook

BUA zai gwangwaje Super Eagles da daloli

Attajirin ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala wasan a shafinsa na Instagram a ranar 10 ga watan Janairun 2026.

Attajirin ya ce zai ba da $100,000 ga kowace kwallon da aka ci a wasan kusa da na karshe da kasar za ta buga. A lissafin da Legit Hausa ta yi, wannan kudi ya kai N149m.

Har ila yau, ya yi alkawarin makudan daloli idan har kasar ta samu nasara a wasan karshe.

Hakan na zuwa ne bayan Najeriya ta doke Algeria da ci kwallo 2 da nema a gasar AFCON da ake yi a kasar Morocco.

A cikin rubutunsa ya ce:

"Taya murna ga ’yan wasan Super Eagles kan gagarumar nasara da suka samu a kan Algeria.
"Kun daga darajar ƙasa, kuma muna alfahari da ku yayin da kuke shirin fafatawa a wasan kusa da na ƙarshe (semi-final).

Kara karanta wannan

Shugaban kwamitin yakin zaben Uba Sani ya rabu da gwamna ya bi El Rufai zuwa ADC

Domin ƙara musu ƙwarin gwiwa, na yi alkawarin ba ’yan wasan $500,000 idan suka lashe wasan kusa da na karshe, tare da ƙarin $50,000 ga kowace kwallo da aka ci."
BUA ta taya Super Eagles murnar doke Algeria
Attajiri a Najeriya, Abdulsamad Rabiu da yan wasan Super Eagles. Hoto: Super Eagles, Abdul Samad Rabiu, CFR, CON.
Source: Getty Images

Super Eagles za su karbi daloli daga BUA

Abdulsamad ya kuma bayyana cewa idan har kungiyar ta kai ga wasan karshe kuma ta yi nasara, zai ba da kyautar $1,000,000.

Attajirin ya ce kuma zai ba da $100,000 ga kowace kwallo da yan wasan suka yi nasarar jefawa a raga domin kara musu kwarin guiwa.

"Idan kuma suka ci wasan ƙarshe (final), ina ƙara alkawarin $1,000,000, tare da $100,000 ga kowace kwallo da aka ci a wasan ƙarshe.
"Ina yi muku fatan samun nasara a ci gaba da daga tutar Najeriya gaba.
"Ku ci gaba da sanya Najeriya alfahari."

- Cewar Abdulsamad Rabiu

'Yan Najeriya sun yi bore kan alawus

Kun ji cewa 'yan wasan Super Eagles da masu horarwa sun kauracewa atisaye da shirin buga wasa na gaba a kasar cin kofin Afirka watau AFCON.

Tawagar 'yan wasan kwallon kafan ta dauki wannan mataki ne saboda kin biyansu alawus din wasanni hudu da suka buga kuma suka samu nasara.

Kara karanta wannan

An yanke wa wani 'dan Najeriya hukuncin kisa a kasar waje, za a rataye shi

Ga masu bibiyar kwallo, an san wannan ba shi ne karo na farko da tawagar Super Eagles ke daukar irin wannan mataki saboda rashin biyansu hakkokinsu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.