AFCON: 'Yan Wasan Najeriya Sun Yi Bore, Sun Gindaya Sharadi kafin Buga Wasa da Algeria

AFCON: 'Yan Wasan Najeriya Sun Yi Bore, Sun Gindaya Sharadi kafin Buga Wasa da Algeria

  • 'Yan wasan Super Eagles da masu horarwa sun kauracewa atisaye da shirin buga wasa na gaba a kasar cin kofin Afirka watau AFCON
  • Tawagar 'yan wasan ta dauki wannan mataki ne saboda kin biyansu alawus din wasanni hudu da suka buga kuma suka samu nasara
  • Wannan ba shi ne karo na farko da tawagar Super Eagles ke daukar irin wannan mataki saboda rashin biyansu hakkokinsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Morocco - Rahotanni sun nuna cewa ’yan wasa da masu horar da tawagar Super Eagles sun ƙi tafiya zuwa Marrakech na ƙasar Morocco domin buga wasa na gaba a gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON).

'Yan wasan sun dauki wannan mataki ne da nufin nuna fushinsu bisa rashin biyansu hakkoki da alawus-alawus dinsu.

Super Eagles.
Yan wasan Najeriya yayin da suka fito domin karawa a gasar AFCON Hoto: Super Eagles
Source: Twitter

Wannan bayani ya fito ne daga ɗan jaridar BBC Africa, Oluwashina Okeleji, ta shafinsa na X, wanda a halin yanzu yake Morocco, kasar da ake buga wasannin kofin AFCON 2026.

Kara karanta wannan

Hadimin Abba ya fadi abin da ke shirin kora 'yan Kwankwasiyya zuwa jam'iyyar APC

Tawagar Super Eagles ta yi bore a AFCON

'Dan jaridar ya ce:

"Yan wasa da masu horar wa na tawagar Najeriya na jiran hakkokinsu daga gwamnati, har yanzu ba a biya su alawus-alawus na nasarorin da suka yi a wasanni hudu, Tanzania, Tunisia, Uganda da Mozambique ba."
"Tawagar Super Eagles ta sha alwashin cewa za ta ci gaba da mai da hankali amma ba za ta yi atisaye ko tafiya zuwa birnin Marrakech ba ranar Alhamis idan ba a warware wannan matsalar ba."

Najeriya ta fara AFCON da kafar dama

Najeriya, wadda tana ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi a gasar, ta yi nasarar lashe dukkan wasanni huɗu da ta buga zuwa yanzu, tare da cin kwallaye mafi yawa a gasar.

Ana sa ran Super Eagles za ta kara da Aljeriya a wasan daf da na kusa da na ƙarshe (Quarter-final) na AFCON 2025 a ranar Asabar da yamma.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa har yanzu ba a biya yan wasan alawus-alawus na wasanni huɗun da aka buga ba.

Kara karanta wannan

Tofa: Osimhen na barazanar barin Super Eagles ana tsaka da wasannin AFCON 2025

Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin koci Eric Chelle ta doke Tanzania, Tunisia da Uganda a matakin rukuni, kafin ta lallasa Mozambique da ci 4–0 a zagayen kasashe 16.

Dalilin 'yan wasan na daukar matakin

Sakamakon rashin warware batun biyan kuɗaɗen, an ce ’yan wasa da tawagar masu horarwa sun dakatar da duk wani shiri na tafiya da atisaye.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba, domin cikin watanni uku da suka gabata, Super Eagles sun taɓa shiga irin wannan yajin aiki kan alawus, cewar rahoton The Nation.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

A watan Nuwamba 2025, sun dakatar da atisaye gabanin wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da Gabon, amma an warware matsalar cikin sa’o’i 24 kacal.

Osimhen ya yi barazanar barin Super Eagles

A wani labarin, kun ji cewa tauraron dan wasan gaba, Victor Osimhen ya yi barazanar daina buga wa Super Eagles wasa bayan hatsaniyarsa da Ademola Lookman.

Wannan dambarwa ta fara ne a fili a lokacin da Najeriya take tsaka da nuna bajinta a wasan ranar Litinin, 5 fa watan Janairu, 2025.

Osimhen ya nuna tsananin fushinsa lokacin da ya ga wasu damarmaki na cin ƙwallo suna lalacewa saboda Lookman da Bruno Onyemaechi sun zaɓi yin wasan nuna gwaninta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262