KAI TSAYE: Yadda Najeriya Ke Fafata Wasa da Tanzaniya a Gasar AFCON 2025

All posts
Key Events
Analysis
Exclusive
28 Posts
Sort by
Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Tanzania ta yi sauyin farko

Msuva ya bar fili, yayin da John ya shigo domin ƙarfafa harin Tanzania.

Minti 63: Najeriya 2-1 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Masudi ya tare harbin Lookman

Najeriya ta yi kyakkyawan farmaki. Simon ya taka rawa a gefen hagu kafin ya zura ƙwallo zuwa Osimhen a cikin akwati.

Osimhen ya saukar wa Lookman ƙwallon da kirji, Lookman ya harba, amma Masudi ya tura ta sama da kwance.

Najeriya na wasa da ƙwarin gwiwa a zagaye na biyu.

Minti 62: Najeriya 2-1 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

An ba Lookman yalon kati

An bai wa dan wasan Najeriya, Lookman, kati bayan ya tunkuyi Miroshi da gangan.

A gefe guda, an sauya Chukwueze da Adams, inda Simon da Bashiru suka shigo.

Minti 59: Najeriya 2-1 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

An dawo da wasa da gaggawa

An jira minti 36 kafin Ajayi ya ci kwallo da kai daga bugun Iwobi.

Sai dai a zagaye na biyu, an ga kwallaye biyu cikin minti biyu kacal. M’Mombwa ya rama, Lookman ya dawo da Najeriya gaba.

Super Eagles na shirin yin sauye-sauye a yanzu.

Minti 58: Najeriya 2-1 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Msuva ya kusa jefa kwallo!

Msuva ya karɓi kyakkyawan fasin da Allarakhia ya tura masa, amma ya harba kwallon waje daga kusa da raga. Sai dai ko da ya ci kwallon, ba za a ba da ta ba, domin an ɗaga tutar offside.

Minti 57: Najeriya 2-1 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

GOAL! Lookman ya sake sanya Najeriya gaba da 2-1

Ana ci gaba da ruwan kwallaye a Fez! Najeriya ta dawo gaba yayin da Lookman ya yi wasa mai kyau da kwallo a wajen akwatin bugun daga kai sai mai tsaron gida, sannan ya saki harbi da kafar hagu, inda kwallon ta shiga raga kai tsaye.

Minti 52: Najeriya 2-1 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Goal! Tanzania 1 - Nigeria

Dan wasan tsakiya na Tanzania ya tsinci kansa a wuri mai kyau, ya karɓi kwallo mai tsawo, sannan ya tura ta ƙasan ragar hagu cikin nasara.

Minti 50: Najeriya 1-1 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

An soke kwallon Osimhen

Osimhen ya karɓi kyakkyawan kwallo daga Adams a cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda ya tura ta ƙasan ragar hagu, amma an soke kwallon saboda ya shiga offside.

Minti 47: Najeriya 1-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Najeriya vs Tanzania: An dawo wasan zagaye na biyu

A cikin ruwan sama mai ƙarfi, ‘yan wasa sun dawo filin wasa domin fara zagaye na biyu.

Idan a yanzu ka shigo: Najeriya na gaba da ci 1-0, bayan bugun kai da Ajayi ya ci a zagaye na farko.

Minti 46: Najeriya 1-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Ana cikin hutun rabin lokaci

Hutun rabin lokaci: Nigeria 1-0 Tanzania

Kwallon da Ajayi ya buga da kai ta shiga raga a minti na 36 ta sa Najeriya ta shiga gaba a wasanta da Tanzaniya, yayin da ake hutun rabin lokaci.

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Masudi ya kare ragar Tanzania sau biyu a jere!

Mai tsaron ragar Tanzania ya fara tsalle hagu ya tare harbin Ndidi mai ƙarfi a kusurwar ƙasa, sannan ya sake tsalle ya tura kwallon Chukwueze sama da saman raga.

Minti 45+1: Najeriya 1-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

An ƙara minti ɗaya

An ƙara ɗan lokaci kaɗan kafin ‘yan wasan su tafi hutun rabin lokaci.

Minti 45: Najeriya 1-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Dama ga Tanzania

Wani hadin kai daga ‘yan wasan Tanzania ya kai kwallo ga Allarakhia, wanda ya karɓa a hagu. Ya harba daga kusurwa, amma Nwabili ya yi kyakkyawan tsayawa ya ceci Najeriya.

Minti 43: Najeriya 1-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Ajayi ya zura kwallo - Najeriya 1 - 0 Tanzania

Dan bayan Najeriya Ajayi ya zura kwallo a ragar Tanzania, wanda ya ba Najeriya nasarar farko a zagayen farko na gasar AFCON.

Ajayi ya yi amfani da kai wajen zura kwallon, wacce golan Tanzania ya gagara tarewa.

36 mins: Nigeria 1-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Osimhen ya sake barar da babbar dama

Iwobi ya aika da kyakkyawar kwallo ya ba Osimhen ta bangaren dama yayin da Najeriya ke kai hari.

Osimhen ya wuce golan, amma ya ja lokaci sosai, hakan ya bai wa Tanzania damar dawowa su kare, daga bisani Super Eagles suka rasa kwallon.

Minti 33: Najeriya 0-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

An shafe rabin awa ana wasa

Chukwueze ya aika kwallo cikin akwatin daga kusurwar dama, inda Masudi ya yi tsalle ya kama kwallon, amma ya buge da ɗan wasan Najeriya.

Ya fadi kasa yana jin zafi, amma daga bisani ya samu damar fitar da kwallon daga hatsari.

Minti 30: Najeriya 0-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Nigeria ta samu bugun kusurwa

Najeriya ta samu bugun kusurwa, wanda zai iya zama kalubale ga Tanzania, la'akari da karfin Osimhen na cin kwallo da kai.

Babu nasara a wannan bugun kusurwa, bayan an doki mai tsaron ragar Tanzania a cikinsa. Wasan ya ci gaba.

30 mins: Nigeria 0-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

An tadiye Osimgen a kusa da ragar Tanzania

An samu dan karamin rikici a kusa da ragar Tanzania, yayin da dan wasan gaban Najeriya, Osimhen ya yi kokarin tafiya da kwallo, amma wani dan wasan bayan Tanzania ya hana shi tare da bugun fuskarsa.

Osimhen ya dan nuna fushinsa, amma mai hura wasa ya shiga tsakani.

Lookman ya harba kwallo sama da Najeriya ta samu freekick bayan an doki Osimhen.

28 mins: Nigeria 0-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Ruwan sama a Fez

An samu ruwan sama a Fez, Morocco, inda har yanzu ba a samu cin ƙwallo ba a wasan.

Najeriya, wacce ta lashe kofin sau uku, ce ke rike da ragamar wasa, amma kada a raina Tanzania a wannan fafatawar.

Minti 23: Najeriya 0-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Tanzania mai rauni amma na nuna Ƙwazo

Chukwueze ya rasa kwallo ga Miroshi, wanda ya nufi yankin bugun daga kai sai mai tsaron raga, amma an tare harbin ƙarshe da ya yi wa kwallon cikin sauƙi.

Wannan kuskure ba kasafai ake gani daga Chukwueze ba, wanda ya kasance muhimmin ginshiƙi a harin Super Eagles zuwa yanzu.

Minti 20: Najeriya 0-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Osimhen ya harba kwallo sama

Osimgen ya samu dama mai kyau, amma ya harba kwallon sama a tazarar yadi 15 daga ragar Tanzania.

Ko da yake, ko da ace ma ya zura kwallo a raga, ba za a ba shi ba, domin tuni lasiman ya daga tuta, alamar Osimhen yana cikin 'offiside'.

17 mins: Nigeria 0-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Kwallo ta bugi karfen raga!

Bugun kusurwa na Chukwueze mai lankwashewa ya samu Adams wanda ya tura kwallo da kai zuwa raga, amma kwallon ta bugi karfen raga ta fita waje.

Minti 14: Najeriya 0-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Ga yawan kujeru, babu masu kallo

An samu ƙarancin masu kallo a filin wasan Fez da ke Morocco a wannan wasa, inda aka ga sassa da dama na kujeru babu mutane.

Sai dai dukkanin tawagogin biyu suna da magoya baya da suka yi tafiya daga ƙasashensu domin halartar gasar.

Minti 11: Najeriya 0-0 Tanzania

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Hasashen ‘yan wasan Najeriya da za su fara shiga fili

Najeriya ba za ta samu damar amfani da 'yan wasan bayanta Benjamin Fredrick da kuma Ola Aina ba sakamakon rauni da suka samu.

Kyaftin din tawagar da aka saba da shi, William Troost-Ekong, ba ya cikin jerin ‘yan wasa bayan da ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasa wasa, inda Wilfred Ndidi ya karbi ragamar jagoranci, kamar yadda muka rahoto.

Rashin ganin ‘yan wasan gaba Victor Boniface da Tolu Arokodare a cikin jerin ‘yan wasan da aka zaba don fafata wasan ya jawo ce-ce-ku-ce.

Hasashen ‘yan wasan farko da za su shiga fili

Nwabili; Osayi-Samuel, Ajayi, Bassey, Sanusi; Chukwueze, Ndidi, Iwobi, Lookman; Osimhen, Adams

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Ina aka shirya gudanar da gasar AFCON 2025?

Ƙasar Morocco ce ke karɓar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON 2025, karo na 35, inda za a buga wasanni a filaye tara da ke cikin birane shida – mafi yawa da aka taɓa samu a tarihin AFCON.

Tun da farko, an bai wa Guinea damar karɓar bakuncin gasar, amma an ƙwace mata hakkin ne saboda damuwa kan shirye-shiryenta, kasancewar tana daga cikin ƙasashen da suka fi fama da talauci a Afirka.

Gasar AFCON ta 2025 ita ce karo na biyu da Morocco ke karɓar bakunci, bayan karon farko da ta yi hakan a 1988, a cewar rahoton Premium Times.

Ga jerin filayen wasa da biranen da za a buga gasar:

Agadir: Filin wasa na Adrar

Casablanca: Stade Mohammed V

Fez: Filin wasan Fez

Marrakesh: Filin wasan Marrakesh

Rabat: Filin wasa na Prince Moulay Abdellah

Rabat: Filin wasa na Moulay Hassan

Rabat: Filin wasan Olympics na Rabat

Rabat: Filin wasa na Al Barid

Tangier: Filin wasan Ibn Batouta

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Najeriya na da sauran dama a gasar Kofin Duniya ta 2026?

A makon da ya gabata, Najeriya ta shigar da korafi ga FIFA, tana zargin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) da saka ‘yan wasa da ba su cancanta ba a wasan da suka fafata na neman tikitin gasar cin kofin duniya ta 2026.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta ce wasu ‘yan wasan da ke da mallakar shaidar zama a ƙasashe biyu sun samu damar bugawa DRC ba tare da cika ka’idojin da ake bukata ba.

Sai dai hukumar kwallon kafar DRC ta musanta wannan zargi, inda har yanzu ake jira a ji ta bakin FIFA. Idan zargin Najeriya ya tabbata, don tana iya samun damar komawa gasar cin kofin duniyar.

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Sauyin koci a tawagar Tanzania

A bangaren Tanzania ma, ba a rasa abubuwan fada da suka shafi kungiyar kwallon kasar ba.

Hukumar kwallon kafa ta Tanzania ta sallami kocinta, Hemed Suleiman, wata guda kacal kafin fara gasar AFCON 2025, inda ta nada Miguel Gamondi a matsayin kocin rikon kwarya na Taifa Stars domin gasar.

Suleiman ne ya jagoranci Tanzania zuwa gasar cin kofin Afirka karo na hudu, tare da kaiwa matakin daf da na kusa da karshe a gasar zakarun nahiyar Afrika (ANC) a bana. Sai dai tawagar ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026.

Kocin Tanzaniya, Miguel Angel Gamondi ya ce lallasa Najeriya a wasansu na farko zai zama tamkar kungiyar kwallonsu ta Taifa Stars ta daga kofin AFCON ne.

Sani Hamza avatar
daga Sani Hamza

Me ya sa Najeriya ta gaza tsallakewa zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026?

Najeriya na daga cikin ƙasashe mafi karfi da suka zo na biyu a rukunonin Afirka guda tara, inda suka samu gurbin fafatawa a matakin playoffs, amma suka sha kashi da ci 4-3 a bugun fanareti a hannun Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC), lamarin da ya hana su kaiwa wasan sharar fage na nahiya da nahiya.

Super Eagles, wadda ta taba halartar gasar cin kofin duniya sau shida, yanzu ta gaza tsallakewa zuwa gasar karo na biyu a jere, a cewar rahoton Aljazeera.

Fara wasannin neman tikiti cikin rauni, sauye-sauyen koci, da kuma rikicin biyan hakkoki sun kasance daga cikin manyan dalilan da suka jawo wa Najeriya wannan babban takaici a hanyar zuwa gasar cin kofin duniya.