Bayan Ritayar Ahmed Musa, An Nada Sabon Kyaftin din Super Eagles
- Tawagar 'yan wasan Super Eagles ta Najeriya ta samu sabon kyaftin bayan ritayar Ahmed Musa da Williams Troost Ekong
- An nada dan wasan tsakiya na Besiktas, Wilfred Ndidi a matsayin wanda zai jagoranci 'yan wasan kungiyar Super Eagles
- Nadin Ndidi na zuwa ne yayin da Najeriya ke shirin fafatawa a gasar cin kofin AFCON na 2025 wanda za a buga a kasar Morocco
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan wasan tsakiya na kungiyar Beşiktaş, Wilfred Ndidi, ya zama sabon kyaftin dkm tawagar Super Eagles.
Wilfred Ndidi mai shekara 29 ya karɓi ragamar jagoranci na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mafi nasara a Afirka.

Source: Getty Images
Super Eagles: Wilfred Ndidi ya zama kyaftin
Sanarwar nadin Wilfred Ndidi na cikin wani saƙo da aka wallafa a shafin X na Super Eagles a ranar Juma’a, 19 ga watan Disamban 2025.
Sanarwar na cewa:
"An naɗa Wilfred Ndidi a matsayin Kyaftin din Super Eagles, kuma ya bayyana cewa wannan nauyi yana da matuƙar muhimmanci a gare shi yayin da Najeriya ke shirin tafiya Morocco.”
Aikin farko na Ndidi shi ne jagorantar Super Eagles, zakarun Afirka sau uku yayin da suke neman samun ɗaukaka a gasar Kofin Ƙasashen Afirka (AFCON) da za a gudanar a Morocco.
Ndidi na bukatar samun hadin kan 'yan wasa
Don cimma wannan buri, dan wasan ya jaddada cewa haɗin kai shi ne mabuɗin nasara, yana kuma ƙarfafa abokan wasansa da su yarda da kansu domin samun nasara a gasar.
"Wannan babbar nauyi ne, kuma da taimakon ’yan wasa, ina ganin komai zai tafi yadda ya kamata."
“Na tattauna da wasu daga cikin ’yan wasa, musamman tsofaffin ’yan wasan. Mun yi magana ne don su fahimci dalilin da ya sa muke nan. Haka kuma muna buƙatar cikakken goyon bayan ma’aikata. Dukkanmu muna tare a wannan tafiya.”
- Wilfred Ndidi
Kyaftin 2 sun yi ritaya a Super Eagles
Naɗin Ndidi ya zo ne bayan ritayar William Troost-Ekong, wanda ya kasance kyaftin din rikon ƙwarya, da kuma Ahmed Musa, wanda shi ne jagoran ƙungiyar a baya.

Source: Instagram
Yayin da Ahmed Musa bai buga wa Najeriya wasa ba tsawon watanni, kuma ya kasance a benci ba tare da an saka shi ba a AFCON na 2023, ritayar Troost-Ekong daga ƙungiyar ƙasa ta ba mutane da dama mamaki.
An sanya sunan Troost-Ekong cikin jerin ’yan wasan da aka fara zaɓa domin AFCON na 2025, amma ya yanke shawarar ajiye taka leda a ƙungiyar ƙasa kafin a fitar da jerin ’yan wasan karshe.
Najeriya na cikin rukunin C a gasar AFCON ta 2025 tare da Tanzania, Uganda da Tunisia. Wasan farko na Super Eagles zai kasance ne a ranar 23 ga watan Disamban 2025.
Ahmed Musa ya yi ritaya daga Super Eagles
A wani labarin kuma, kun ji cewa shahararren dan wasan kwallon kafa, Ahmed Musa, ya yi ritaya daga bugawa Super Eagles wasa.
Shahararren dan wasan ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai yi ritaya daga bugawa Super Eagles ta Najeriya wasa.
Ahmed Musa ya yi ritaya ne bayan ya zama dan wasan da ya fi taka leda ga Najeriya, inda ya buga wasa har sau 111.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


