Wasanni Nawa Ya Rage wa Najeriya Ta Shiga Gasar Cin Kofin Duniya? Bayanai Sun Fito

Wasanni Nawa Ya Rage wa Najeriya Ta Shiga Gasar Cin Kofin Duniya? Bayanai Sun Fito

  • Najeriya ta doke Gabon 4-1 a karin lokaci, ta tsallaka wasan neman gurbin World Cup inda za ta kece raini da DR Congo
  • Kafin ta samu tikitin 2026, Super Eagles za su buga akalla wasa ɗaya, amma zai iya zama biyu dangane da matsayinsu a FIFA
  • Idan Najeriya ta kasance cikin ƙasashen da suka fi kowa daraja a zaben Mexico, sai ta yi wasa guda tak domin samun gurbi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Najeriya ta samu nasara a burinta na shiga gasar cin kofin duniya bayan ta lallasa Gabon da ci 4-1 a karin lokaci, a wasan share fage na takwas da aka buga a Morocco.

Wannan nasara ta bai wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles damar buga wasan karshe na play-off da kasar DR Congo a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Bahaushe ya sha ruwan yabo bayan mayar da wayar iPhone da ya tsinta a kasuwa

Najeriya ta doke Gabon, inda za ta kara da DR Congo a ranar Lahadi. Akwai wasanni 3 a gabanta.
Hoton kofin duniya da na 'yan wasan kwallon kafar Najeriya. Hoto: @NGSuperEagles
Source: Getty Images

Najeriyar ta rasa samun gurbi kai tsaye ne bayan Afirka ta Kudu ta yi nasara a wasanta na karshe, wanda ya sa Super Eagles ta tsaya a matsayi na biyu a rukuninsu, in ji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarar Najeriya zuwa wasanta da DR Congo

Nasarar 4-0 da suka yi kan Benin ta sa Najeriyar ta samu tazara tsakaninta da Burkina Faso a bambancin kwallaye, wanda ya ba ta damar shiga karamin gasa ta kungiyoyi biyu mafi hazaka a rukunai.

Bisa jerin darajar FIFA, Najeriya ce ta fi kowa matsayi (41), abin da ya sa aka tura ta ta fafata da Gabon (77) a wasan dab da karshe.

Chidera Ejuke da Victor Osimhen ne suka jagoranci cin kwallon da ta bai wa Najeriya tikiti na zuwa wasan karshe, yayin da DR Congo ta doke Cameroon da ci 1-0 a wasan da Chancel Mbemba ya zura kwallo a minti na 91.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Gwamnatin Tinubu ta fadi halin da ake ciki kan tattaunawa da Amurka

Wasa nawa suka rage kafin Najeriya ta shiga gasar?

A zahiri, akwai yiwuwar Najeriya ta yi wasa guda tak, ko kuma wasa biyu kafin ta samu gurbin shiga wasannin gasar cin kofin duniya na 2026, in ji rahoton BBC.

1. Wasan karshe na sharar fage – Najeriya vs DR Congo

Za a buga wannan wasan ne a ranar Lahadi, 16 ga Nuwamba, a Morocco. Wanda ya yi nasara zai wuce zuwa wasannin sharar fage na Inter-Confederation, watau nahiyo da naihiyoyi.

2. Inter-Confederation – Mexico, Maris 2026

A wannan mataki, kasashe shida daga nahiyoyi biyar za su fafata domin samun gurabe biyu na karshe biyu na shiga gasar cin kofin duniya.

Najeriya na bukatar ta doke DR Congo da wasu kasashe 2 a wasanninsu na nan gaba
Hoton 'yan wasan kwallon kafar Super Eagles da na kocinsu, Eric Chelle. Hoto: @NGSuperEagles, @Eric_chelle1
Source: Getty Images

Me zai sa Najeriya ta yi wasa guda ko biyu?

  • Idan Najeriya ta kasance cikin ƙasashe biyu mafi matsayi: Za ta tsallake wasan kusa da na karshe, ta buga wasan karshe guda ɗaya kawai – idan ta ci, ta tsallake zuwa gasar.
  • Idan ba ta cikin manyan kasashe biyu: Za ta buga wasan kusa da na karshe, sannan ta buga wasan karshe, kenan za ta yi wasanni biyu.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin Birtaniya, gwamnatin Tinubu ta fitar da sakamakon yaki da ta'addanci na 2025

Abin da wannan ke nufi:

Najeriya ta riga ta yi nasara a wasan farko da ta buga da Gabon. Yanzu idan ta doke DR Congo, za ta je Mexico.

A Mexico kuma, sai ta ci wasa ɗaya ko biyu don ta samu gurbi a gasar cin kofin duniya, karon farko tun 2018.

Messi ya magantu kan wasannin kofin duniya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ɗan wasan Argentina, Lionel Messi, ya bayyana cewa yana fatan taka leda a gasar cin kofin duniya ta 2026.

Lionel Messi ya ce zai duba lafiyarsa da yanayin jikinsa kafin ya yanke shawarar karshe kan shiga gasar a shekara mai zuwa.

Ya bayyana cewa buga gasar a karo na gaba na cikin abubuwan da yake fata a rayuwarsa bayan nasarar da suka samu a Qatar a 2022.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com