Gbenga Daniel: Yadda Sanata Ya Ci Dunduniyar APC a Zaben Cike Gurbi

Gbenga Daniel: Yadda Sanata Ya Ci Dunduniyar APC a Zaben Cike Gurbi

  • Wani rahoto ya nuna yadda Gbenga Daniel ya umurci magoya bayansa su ci dunduniyar jam'iyyar APC
  • Jam'iyyar APC ta tunkari sanatan mai wakiltar Ogun ta Gabas don ya kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa
  • APC ta bayyana hakan a matsayin cin amana, inda ta dauki matakin ladabtarwa a kansa da wani na kusa da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ogun – Sanata Gbenga Daniel, wanda ke wakiltar Ogun ta gabas, ya shiga cikin rikici bayan an zarge shi da cin dunduniyar jam'iyyar APC.

Ana zargin dai sanatan ya bukaci magoya bayansa su marawa 'yar takarar jam'iyyar PDP baya, maimakon ta APC.

APC ta dakatar da Sanata Gbenga Daniel
Hoton Sanata Gbenga Daniel a zauren majalisa Hoto: Gbenga Daniel
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa Sanata Gbenga Daniel ya bukaci magoya bayansa su goyi bayan Bolarinwa Oluwole na PDP a zaben cike gurbi na Ikenne/Sagamu/Remo ta Arewa da aka gudanar a watan Agusta.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Matasan Arewa sun taso El Rufai a gaba, an ji dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaben ya biyo bayan mutuwar tsohuwar 'yar majalisar wakilai ta yankin, Adewunmi Onanuga, a watan Janairu.

Wane zargi ake yi wa Sanatan APC?

Kwanaki kafin zaben, Gbenga Daniel ya aika da sakonni ta WhatsApp ga magoya bayansa yana cewa su “tattara mutane su kada kuri’a kamar yadda aka yi a baya” su zabi Bolarinwa Oluwole kan 'yar takarar APC, Adesola Elegbeji.

Jaridar ta ce wata majiya ta bayyana cewa sanatan wanda a lokacin baya cikin kasar nan, ya umarci mutanensa da su goyi bayan PDP kamar yadda su ka yi a zaben baya, tare da yi musu alkawarin ba su cikakken goyon baya idan ya dawo.

"Ku tattara mutanenmu su kada kuri'a kamar yadda muka yi a baya. Kodayaushe zan goyi bayan PDP."

- Gbenga Daniel

Sai dai daga bisani ya goge sakon bayan wasu shugabannin APC sun tambaye shi, inda ya jingina laifin kan AI.

Majiyoyi sun ce bayan zabensa, a sirrance Gbenga Daniel ya goyi bayan PDP a zaben gwamnan 2023, inda ya juyawa APC baya duk da cewa yana daya daga cikin manyan jiga-jiganta a Ogun.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya gaji da zama haka, zai nemi takarar gwamna karkashin APC

Sun kara da cewa shugabannin jam'iyyar APC wadanda su ka samu labarin umarnin da sanatan ya ba magoya bayansa kan zaben cike gurbin, sun girgiza inda su ka bayyana hakan a matsayin cin amana.

APC ta dauki mataki

A ranar 17 ga Agustan 2025, INEC ta sanar da Adesola Elegbeji ta APC a matsayin wadda ta yi nasara da kuri’u 41,237, inda ta doke Oluwole na PDP wadda ta samu kuri’u 14,324.

Bayan kwanaki uku, a ranar 19 ga Agustan 2025, APC ta dakatar da Gbenga Daniel da wani na kusa da shi, Kunle Folarin, har sai baba ta gani bisa zargin cin amanar jam’iyya.

A cikin wata sanarwa, APC ta ce an kafa kwamitin ladabtarwa a Sagamu don bincike, inda aka gayyaci Daniel da Folarin su kare kansu, amma suka gaza bayyana ko tura rubutaccen bayanin kariya.

APC ta dakatar da Sanata Gbenga Daniel
Hoton Sanata Gbenga Daniel na jam'iyyar APC Hoto: @Gbengadaniel
Source: Twitter

Sanata Gbenga Daniel bai yi tsokaci ba

Jaridar ta ce an tuntubi sanatan domin jin ta bakinsa, amma bai amsa kiran waya ko sakonnin da aka tura masa ba.

Hakan ya kara hura wutar ce-ce-ku-ce kan matsayinsa a cikin jam’iyyar da kuma siyasar jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Kusan watanni 2 bayan ya rasu, an dauko batun ayyuka da Buhari ya gaza yi a Arewa

Gbenga Daniel ya magantu kan dakatar da shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Ogun ta Gabas, Gbenga Daniel, ya yi magana kan dakatarwar da aka yi masa daga APC.

Mai magana da yawun sanatan, ya bayyana cewa babu wata takarda a hukumance da APC ta aikewa tsohon gwamnan.

Steve Oliyide ya bayyana cewa a kafafen sada zumunta kawai su ka ci karo da batun dakatar da sanatan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng