"Bai Damu ba": Peter Obi Ya Ragargaji Tinubu yayin da Ya Shirya Tafiya Kasashen Waje
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya nuna rashin jin dadinsa kan tafiyar da Shugaba Bola Tinubu zai yi
- Peter Obi ya bayyana cewa bai kamata shugaban kasan ya tafi kasashen waje ba da halin da kasar nan ke ciki
- Ya nuna cewa maimakon tafiya zuwa kasashen waje, kamata ya yi ya zagaya jihohin kasar nan domin ganin da jama'a ke ciki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasan a zaben 2023, Peter Obi, ya ragargaji mai girma Bola Tinubu.
Jagoran Obidient, Peter Obi ya soki shugaban kasan ne kan tafiyar da zai yi zuwa kasashen Japan da Brazil.

Asali: Facebook
Peter Obi ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Alhamis 14 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan
Jerin sunaye: Shugaba Tinubu ya amince da kafa sababbin jami'o'i 9 a Kaduna da wasu jihohi 7
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya caccaki Bola Tinubu
Tsohon dan takarar shugaban kasan ya bayyana cewa Tinubu bai damu da halin da kasar nan ke ciki ba, shiyasa zai tsallake ya tafi kasashen waje.
"A cikin wannan mawuyacin halin da kasarmu ke ciki a kowane fanni, muna da shugaban kasa wanda ya nuna rashin damuwa da halin da muke ciki."
- Peter Obi
Peter Obi ya kuma soki kwanakin da shugaban kasan zai kwashe a yayin tafiyar tasa.
"Lamarin yana tayar da hankali matuka. Shugaban kasa, wanda bai ga darajar ziyartar jihohinmu da ke cikin tashin hankali ba, yana samun farin ciki a tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje a kowace karamar gayyata ko uzuri."
"Sau da dama ma yana tafiya kwanaki da dama kafin ma taron da aka gayyace shi."
"Ya kamata yawon da yake yi ya fi karkata zuwa jihohin da ke cikin matsala a gida, domin ya zauna a kasa, ya ɗauki matakan gaggawa na rage wahalar jama’a, maimakon tarurrukan ƙasashen waje da ba su kawo wani gagarumin ci gaba a kan matsalolinmu ba."
"Idan tafiyar ta zama dole ma, za ta iya ɗaukar 'yan kwanaki kaɗan maimakon tsawaita zama a waje ba gaira ba dalili."
"Abin da ƙasarmu ke buƙata yanzu shi ne tsaron rayuka da dukiyoyi, daidaituwar tattalin arziki, da tabbatar da mutane suna da abin ci a teburinsu."
"Shugaban kasa na shirin yin tafiyar kwanaki 12 daga yau, alhali idan ya zama dole, ya kamata ta zama tafiyar kwanaki biyar kawai, domin taron da aka gayyace shi a Japan zai fara ne a ranar 20 ga watan Agusta."
- Peter Obi

Asali: Facebook
Peter Obi ya ba Tinubu shawara
Peter Obi ya kuma bukaci Shugaba Tinubu da ya fara kai ziyarar gani da ido a jihohin kasar nan, domin duba halin da jama'a suke ciki.
"Dole ne shugaban kasa ya fara yawon ziyartar jihohin kasar nan cikin gaggawa da irin kuzarin da yake nuna wa wajen yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje kowane wata."

Kara karanta wannan
"Ina da tabbaci," Bwala ya hango yadda za ta kaya tsakanin Jonathan da Tinubu a 2027
"Wadannan ziyarce-ziyarce za su ba shi damar gani da ido, jin ta bakin mutane, da fahimtar irin halin da ‘yan ƙasa ke ciki."
"Ko da yake ‘yan Najeriya sun san cewa ba za a magance manyan matsalolinmu cikin dare ɗaya ba, suna so su ga kaso 100% na kokari da sadaukarwa don warware su."
"Abu mafi muhimmanci, shugaban ƙasa ya kamata ya fahimci cewa ba ɗan yawon shakatawa ba ne, amma shugaba ne na kasa mai cike da matsaloli."
- Peter Obi
Ibrahim Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa tafiye-tafiyen da shugaban kasan yake sun yi yawa.
"A bayyane yake shugaban kasa ta yawon shi kawai yake yi. Ana fama da matsalar tsaro amma ya dauki kafa ya tafi kasar waje."
"Wannan tafiyar sai ya kwashe kwanaki kafin ya dawo, kuma ba a gayawa 'yan Najeriya abin da zai tsayar da shi a Dubai ba."
- Ibrahim Kabir
Bwala: 'Tinubu zai samu kuri'u a yankin Obi'

Kara karanta wannan
Ana jita jitar rashin lafiya, Tinubu ya yi magana, ya fadi gwamnonin da zai yi alaƙa da su
A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu, zai samu kuri'u a yankin Peter Obi.
Daniel Bwala ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu kuri'u masu yawa fiye da wadanda ya samu a zaben 2023 a jihohin Kudu maso Gabas.
Hadimin shugaban kasan ya bayyana cewa Peter Obi ba zai hana Tinubu samun kuri'u a yankin ba, domin tasirinsa ya ragu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng