Super Falcons: Ana Hayaniya kan Kyautar Tinubu, Fintiri Ya ba da Gida, Miliyoyi ga Kocinsu
- Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya gwangwaje cocin kocin Super Falcons, Justine Madugu da kyaututtuka
- Fintiri ya ba Madugu gida da N50m saboda jagorantar Najeriya ta lashe kofin WAFCON da aka gudanar a Morocco
- A taron karɓarsa a Yola, gwamnan ya yaba da ƙwarewar Madugu, ya ce nasararsa ta kawowa Najeriya da jihar Adamawa daraja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya ba cocin Super Falcons kyaututtuka bayan lashe gasar WAFCON
Fintiri ya ba kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya, Justine Madugu, gida mai ɗakuna uku da kuɗi N50m.

Source: Facebook
Fintiri ya ba da kyautar N50m, gida ga Madugu
Gwamna Fintiri shi ya tabbatar da haka a shafin X lokacin da ya ba da kyautar yayin da ya karbi bakuncinsa a birnin Yola da ke jihar.

Kara karanta wannan
Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi hakan ne saboda rawar da ya taka wajen jagorantar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya zuwa nasarar lashe kofin WAFCON 2025.
Madugu wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Numan ne, ya samu tarbar a gidan gwamnati da ke Yola ranar Juma’a.
Ya ce:
“Lokacin da aka naɗa shi koci, ban yi shakka da ƙwazonsa ba. Ya kawo daraja ga Najeriya da jihar Adamawa.”
Fintiri ya fadi abin da ya ji da nasarar
Gwamnan ya ce nasarar Super Falcons karo na 10 a WAFCON babban abin alfahari ne ga Najeriya da kuma al’ummar Adamawa.
Yayin da yake mika kyautar gida da N50m, Fintiri ya ƙara tabbatar da kudirin gwamnatinsa wajen bunƙasa harkar wasanni.
Ya bayyana cewa gwamnati ta gina filayen wasa a wasu ƙananan hukumomi, da filin wasa na zamani.
“Ina so ka dawo gida ka taimaka wajen haɓaka matasa. Nasararka za ta zamo haske ga sababbin ’yan wasa."
- Cewar Fintiri

Source: Twitter
Kocin Super Falcons ya yi godiya ga Fintiri
Madugu ya bayyana godiyarsa bisa wannan karramawa da tarbar da gwamnatin Adamawa ta yi masa, Vanguard ta ruwaito.
Ya ce:
“Abin da ke faruwa yau na daga cikin mafi girma a rayuwata. Na gode da wannan yabo da karramawa.
“Lokacin da na karɓi aikin nan, na ɗauke shi a matsayin ƙalubale domin nuna cewa Arewacin Najeriya ma na iya jagoranci.”
Madugu ya bayyana cewa Adamawa ta ba da gudummawa sosai ga harkar wasanni, inda ’yan wasa sama da 20 ke wakiltar Najeriya.
Sai dai ya roƙi gwamnati da ta ƙara mayar da hankali kan haɓaka wasan mata, yana mai cewa wasu al’adu da addini na hana ci gaba.
Tinubu ya gwangwaje Super Falcons da kyaututtuka
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya karrama ‘yan wasan Super Falcons da kyautar $100,000 da gidaje bayan sun lashe kofin WAFCON na 2025.
Shugaban kasar ya kuma ba 'yan wasan lambar girmamawa ta OON a liyafar da aka shirya masu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Najeriya ta doke Morocco da ci 3-2 inda Esther, Folashade da Echegini suka zura kwallo uku bayan Morocco ta fara jan ragamar wasan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

