Super Falcons: Yadda Tinubu Ya Shiga Fargabar Hawan Jini a Fadar Shugaban Kasa

Super Falcons: Yadda Tinubu Ya Shiga Fargabar Hawan Jini a Fadar Shugaban Kasa

  • Shugaba Bola Tinubu ya ce a farko ya ki kallon wasan karshe na WAFCON saboda gudun fargaba da hawan jini
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake karɓar tawagar Super Falcons a fadar shugaban ƙasa da yammacin ranar Litinin
  • Bola Tinubu ya karrama ƴan wasan Najeriya da lambobin girmamawa saboda nasarar da suka samu a kasar Morocco

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ya ƙi kallon wasan karshe na gasar cin kofin Afrika na mata (WAFCON) domin gudun hauhawar jinin sa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi tawagar ƙungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Yayin da Bola Tinubu ya karbi matan Najeriya da suka ci kofi a Maroko
Yayin da Bola Tinubu ya karbi matan Najeriya da suka ci kofi a Maroko. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Rahoton Channels TV ya nuna cewa yce duk da ƙin kallon wasan da farko, daga bisani an tilasta masa kallon shi, lamarin da ya sa ya shiga wani irin yanayi na tsananin ɗoki da fargaba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gwangwaje ƴan wasan Super Falcons, ya ba kowa kyautar N152.8m da gidaje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce ya ji tsoron hawan jini

Yayin da ya ke bayani a fadar shugaban kasa bayan dawowar 'yan wasan Najeriya daga kasar Morocco, shugaba Tinubu ya ce:

“Gaskiya ban fara kallon wasan ba. Ban son tashin hankali da hawan jini. Amma sai wasu suka shigo ɗakin nawa suka kunna talabijin, suka saka tashar da ake nuna wasan.”

Ya cigaba da cewa:

“Lokacin da aka ci mu 2-0, na shiga firgici sosai. Amma sai da muka ci kwallo ɗaya, na ji zuciyata ta ta fara sakewa. Kuma na san zuciyar yawancin ‘yan Najeriya ma ta ɗan kwanta.”

Yadda aka yi wa Tinubu girki a ranar

Shugaban kasar ya bayyana cewa kallon wasan ya kusa sanya uwar gidansa ta makara da shirya masa abincin dare, inda ya ce:

“Uwargida tana cikin girki a madafi, sai kawai ta fito da gudu tana cewa mun yi nasara. Na ce mata ‘har yanzu ba a gama ba.’

Kara karanta wannan

An daure wanda ya kagi labarin rasuwar Bola Tinubu a mummunan yanayi

"Sai da aka busa usur din ƙarshen wasa ne kawai muka tabbatar da mun yi nasara.”

Tinubu ya bayyana cewa irin jajircewar da tawagar Super Falcons ta nuna ta sanya shi cikin farin ciki da alfahari, inda ya bayyana su a matsayin ƙungiya mai jarumta da ƙwazo.

Wasu daga cikin 'yan wasan Najeriya na taka leda
Wasu daga cikin 'yan wasan Najeriya na taka leda. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Tinubu ya yi farinciki da nasarar Najeriya

Shugaban ya ce nasarar da ‘yan matan suka samu ba wai kawai ta faranta masa rai ba ce, har da ɗaukacin al’ummar Najeriya.

Ya ce:

“Wannan nasara ta sa kowa ya ji daɗi a cikin gida da wajen Najeriya. Abin alfahari ne mu samu irin wannan tawaga da ke nuna karfin hali da jajircewa a kowanne mataki.”

Vanguard ta wallafa cewa bayan jawabin sa, Shugaba Tinubu ya karrama ‘yan wasan da lambobin girma na kasa, inda ya ba kowannensu lambar OON.

Tarihin alakar Bola Tinubu da Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi bayani game da alakar shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

"Labarin ƙarya," An ji gaskiyar abin da ya faru kan batun ganawar Tinubu da Kwankwaso

Hadimin shugaba Bola Tinubu, Abdulaziz Abdulaziz ya bayyana cewa tun shekarar 1993 suka fara aiki tare a majalisar kasa.

Ya bayyana cewa babu laifi idan 'yan siyasar suka sake kulla alaka domin cimma wata manufa a yanzu lura da abin da ya faru a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng