Manchester United Ta Naɗa Sabon Koci, Ruben Amorin Kwanaki da Korar Ten Hag
- Rahotanni na nuna kungiyar kwallon kafar Manchester United ta naɗa sabon koci da zai jagoranci kungiyar zuwa shekaru masu zuwa
- Ruben Amorin ne sabon kocin Manchester United kuma ya baro aikin horas da yan wasa ne daga kungiyar Sporting zuwa Old Trafford
- Manchester United ta bayyana shekarun da Ruben Amorin zai dauka yana horas mata da yan wasa da kuma lokacin da zai fara aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
United Kingdom - Kungiyar kwallon kafar Manchester United ta sanar da cewa Ruben Amorin ne zai maye gurbin kocin da ta kora.
Ruben Amorin ya zamo na shida a cikin jerin masu horas da yan wasa a Man United tun bayan tafiyar Sir Alex Ferguson a 2013.
Rahoton BBC ya nuna cewa Manchester United ta yi na'am da cewa Ruben Amorin zai fitar wa kungiyar kitse a wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manchester United ta naɗa sabon koci
Kungiyar kwallon kafar Manchester United ta sanar da nada Ruben Amorin a matsayin sabon mai horas da yan wasa.
Ruben Amorin ne zai maye gurbin Erik Ten Hag bayan korarsa da Manchester United ta yi a wannan makon.
Manchester United ta bayyana cewa Ruben Amorin ya fito ne daga kasar Portugal kuma yana da shekaru 39 da haihuwa.
Ruben Amorin zai fara aiki a Man United
Punch ta wallafa cewa Amorin zai fara aiki a Manchester United ne a ranar 11 ga watan Nuwamba bayan ya taho daga kungiyar Sporting.
A ranar 24 ga Nuwamba Amorin zai fara jagorantar wasa a gasar Premier inda Man United za ta kara da Ipswich.
A ranar 28 ga Nuwamba Man United za ta karbi baƙuncin gasar Europa wanda shi ne zai kasance wasan Amorin na farko a Old Trafford.
A nawa aka kawo sabon kocin Man United?
Kungiyar kwallon kafar Sporting ta tabbatar da cewa ta sakin Ruben Amorin ga Manchester United ne a kan £9.25m.
Ana sa ran Amorin zai cigaba da horas da yan kwallon kafar Manchester United har zuwa watan Yunin shekarar 2027.
An kashe mai goyon bayan Man United
A wani rahoton, kun ji cewa an shiga rudani bayan wani dan kungiyar Arsenal ya yi ajalin magoyin bayan Manchester United a kasar Uganda.
Lamarin ya faru ne a kasar Uganda bayan dan Arsenal ya hallaka magoyin bayan Manchester United mai suna Benjamin Okello.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng