Kopa 2024: Matashin Dan Kwallon Barcelona Ya Lashe Babbar Kyauta Ta Duniya
- Lamine Yamal ya lashe kyautar gwarzon matashin ɗan kwallo watau Kopa Tropy 2024 a birnin Faris na ƙasar Faransa
- Matashin ɗan kwallon wanda ke taka leda a Barcelona ya zama na farko da ya ci kyautar a ƙasa da shekaru 18
- An ba Yamal wannan kyauta ne a wurin biki ba da Ballon D'Or ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba, 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Paris, France - Tauraron dan kwallon Barcelona, Lamine Yamal ya lashe kyautar Kopa Trophy 2024 a bikin bada kyautar Ballon d’Or a birnin Paris a ƙasar Faransa.
Hakan ya nuna cewa Yamal shi ne matashin ɗan kwallon da ya fi kowa iya taka leda a shekarar 2024.
Fitaccen ɗan jaridar nan mai kawo ingantattaun labaran kwallon kafa, Fabrizio Romano ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yamal ya lashe kyautar King Trophy 2024
Lamine Yamal, ɗan shekara 16 a duniya ya lashe kyautar gwarzon matashin dan kwallo watau Kopa Trophy 2024 ne saboda ƙoƙarin da ya yi a Barcelona da ƙasar Sifaniya.
Yamal ya lallasa manyan abokan karawarsa, Ader Guler wanda ya zo na biyu, Kobbie Mainoo na uku, Savinho na huɗu da Pau Cubarsi wanda ya zo na biyar
Matashin ɗan wasan ya kuma kafa tarihin zama ɗan kwallon da bai kai shekara 18 ba kuma ya ci kyautar Kopa Trophy, wanda ake ba matasa ƴan ƙasa da shekara 21.
Yamal ya yi jawabi a bayan lashe kyauta
Yamal ya ce:
“Abin alfahari ne da na taka wannan matsayi. Na sadaukar da wannan kyautar ga mahaifiyata, kakata, ga ƙungiyar Barcelona, masu horarwa da dukkan waɗanda suka mara mani baya."
Yamal ya taimaka wa Spain ta lashe gasar Euro 2024 a lokacin bazara kuma a halin yanzu Barcelona ce ke kan gaba a teburin La Liga bayan da ta fara kakar wasa ta ƙafar dama.
Manyan ƴan kwallon da suka yi ritaya a 2024
Ku na da labarin a kakar wasa ta bana wato shekarar 2024 an samu yan wasan ƙwallon ƙafa da dama da suka yi ritaya daga buga tamola.
Hakan bai rasa nasaba da yawan shekarun da suke da shi wanda ka iya kawo musu cikas a harkokin wasanni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng