'Yan Wasan Kano Pillars Sun Yi Hatsari a Jos, An Bayyana Halin da Suke Ciki

'Yan Wasan Kano Pillars Sun Yi Hatsari a Jos, An Bayyana Halin da Suke Ciki

  • Rahoto ya nuna 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars sun yi hatsari a kan hanyarsu ta zuwa filin wasan Jos
  • An rahoto cewa tawagar Kano Pillars ta 'yan kasa da shekaru 19 ta yi hatsarin motar ne yau Talata, 22 ga watan Oktoba
  • 'Yan wasa da dama tare da direban motar sun samu raunuka yayin da kwamitin watsa labaran tawagar ya fitar da karin bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Motar da ta kwaso 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, tawagar 'yan kasa da shekaru 19 ta samu hatsari.

An rahoto cewa 'yan wasa da dama sun samu raunuka sakamakon hatsarin da ya rutsa da su a ranar Talata, 22 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

Motar da ta kwaso tawagar Kano Pillars ta yi hatsari a Jos
'Yan wasan Kano Pillas sun yi hatsarin mota a Jos. Hoto: @pillarsfc/X
Asali: UGC

Yan wasan Kano Pillars sun yi hatsari

Rahoton da Jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa motar tawagar Kano Pillars ta yi hatsari a hanyarta ta kai 'yan wasan zuwa sabon filin wasanni na Jos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan wasan za su je filin wasan Jos ne domin buga wasansu na biyar a gasar zakarun matasa 'yan kasa da shekaru 19 (U-19 YL).

"Cikin bakin ciki ne muke sanar da cewa motar bas din kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars (U-19) ta yi hatsarin mota a safiyar yau."

- A cewar sanarwar da Kano Pillars ta fitar a shafinta na X.

Tawagar Kano Pillars za ta buga wasan ne da tawagar kungiyar kwallon kafa ta Plateau United.

Haalin da 'yan wasan Kano Pillars ke ciki

A cewar kwamitin watsa labaran Kano Pillars (U-19), direban motar da 'yan wasa da dama sun samu raunuka kuma an garzaya da su asibiti domin ba su kulawa.

Kara karanta wannan

Gyaran tattalin arziki: Manyan nasarori 5 da gwamnatin Tinubu ta samu a 2024

"Cikin hukuncin Allah SWT, ba a samu asarar rayuka zuwa yanzu da nake ba da wannan rahoto ba, tawagar jami'an kiwon lafiya na ba 'yan wasan kulawa.
"Muna jajantawa wadanda hatsarin ya shafa kuma za mu bayar da karin bayanai nan gaba kadan."

- A cewar kwamitin watsa labaran.

Abba ya kori shugabannin Kano Pillars

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya runtuma kora a hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Gwamna Abba ya sanya hannu kan korar shugabannin Kano Pillars ne bayan da kwamishinan wasannin jihar, Mustapha Kwankwaso ya sallame su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.