‘Mun Samu Matsala a Kasarsu,’ Libya Ta yi Bayani kan ‘Azabtar’ da Yan Kwallon Najeriya

‘Mun Samu Matsala a Kasarsu,’ Libya Ta yi Bayani kan ‘Azabtar’ da Yan Kwallon Najeriya

  • An wayi gari a yau Litinin da labarin yan kwallon Najeriya sun makale a filin jirgin saman kasar Libya daga zuwa buga wasa
  • Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce wanda al'ummar kasar nan suka koka kan cewa ba a girmama yan kwallonsu na Super Eagles ba
  • Sai dai hukumar kwallon kafar Libya ta fitar da sanarwar da ta wanke kanta daga zargin cewa ta wahalar da yan Najeriya ne da gangan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Libya - Hukumar kwallon kafa a kasar Libya ta yi bayani kan makalewar yan kwallon Najeriya a filin jirgin sama.

Hukumar LFF ta ce babu gaskiya cikin zargin cewa ta wahalar da yan kwallon Najeriya ne da gangan.

Kara karanta wannan

Likitoci, lauyoyi sun nemi Tinubu ya warware matakin NNPCL da fetur ya kai N1030

Yan Najeriya
An gano dalilin makalewar yan Najeriya a Libya. Hoto: @WTroostEkong
Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa hukumar FFF ta ce ba ramakon gayya ta yi ba duk da cewa ita ma ta fuskanci matsala a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan kwallon Najeriya sun makale a Libya

A safiyar yau ne Kyaftin din yan kwallon Najeriya ya wallafa a shafinsa na X cewa yan wasan Najeriya sun makale a filin jirgin saman Libya.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce yayin da al'ummar Najeriya suka nuna rashin jin dadi kan abin da suka kira da cin fuska.

Libya: Dalilin makalewar yan kwallon Najeriya

Hukumar kwallon kafar Libya, LFF ta ce yan kwallon Najeriya sun makale a filin jirgin sama ne saboda dalilai da suka shafi sufuri.

The Cable ta wallafa cewa LFF ta ce lamarin zai iya faruwa a kowace kasa kuma ba wai da gangan suka yi wa yan kwallon Najeriya ba saboda suna girmama su.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fadi lokacin fita a kangi, ya kawo hanyoyin magance matsaloli

Yan Libya sun makale a Najeriya

Hukumar LFF ta ce yan kwallonta da suka zo Najeriya sun fuskanci matsaloli irin haka amma su ba su yi zargin da gangan aka musu hakan ba.

A yanzu haka dai yan kwallon Najeriya sun ce za su fice daga kasar Libya ba tare da buga wasa ba saboda matsalar da suka fuskanta.

An kama dan kwallo da zargin sata

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni sun ce an kama wani dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a kasar Spain bisa zargin sata.

An ce an kama Matheus Nunes ne a gidan rawa na La Riviera da ke Madrid a ranar 8 ga watan Satumba bisa zargin satar wayar wani mutum.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng