Osimhen Ya Amince da Tayin Chelsea Na Karbar Albashin Naira Miliyan 617 duk Mako

Osimhen Ya Amince da Tayin Chelsea Na Karbar Albashin Naira Miliyan 617 duk Mako

  • Rahotanni sun bayyana cewa an cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da dan wasan Najeriya, Victor Osimhen
  • Rahotanni sun bayyana cewa Osimhen ya amince da tayin Chelsea na karbar albashin €350,000 (kimanin N617.4m) a kowane mako
  • Sai dai an ce har yanzu ba a kai karshen maganar ba, inda kungiyar kwallon kafa ta Al Ahli da ke Saudiya ke ci gaba da zawarcin Osimhen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Da alama tataburzar da ake kan yi kan cinikayyar fitaccen dan wasan ƙwallon gaba na Super Eagles, Victor Osimhen ta kusa zuwa karshe.

An ce Osimhen ya amince da tayin da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi masa na biyansa albashin €350,000 (N617.4m) duk mako.

Kara karanta wannan

Osimhen ya rasa gurbinsa a Napoli, an kwace lambar rigarsa, yana neman mafita

An cimma yarjejeniya tsakanin Victor Osimhen da Chelsea
Victor Osimhen ya amince da tayin Chelsea na karbar albashin Yuro 350,000. Hoto: @victorosimhen9, @ChelseaFC
Asali: Getty Images

Dan jaridan Najeriya da hukumar kwallon UEFA ta amince da shi, Oma Akatugba ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chelsea za ta biya Osimhen €350,000

Akatugba ya bayyana cewa da farko Osimhen ya bukaci Chelsea ta rika biyansa albashin €500,000 duk mako, amma hakan bai yiwu ba.

Ya ce an yi ta ciniki tsakanin kungiyar kwallon kafar da dan wasan, har dai aka cimma matsaya kan albashin €350,000 a duk mako.

Sai dai dan jaridan ya jaddada cewa har yanzu ba a kai karshen maganar ba, inda kungiyar kwallon kafa ta Al Ahli da ke Saudiya ke ci gaba da zawarcin Osimhen.

Tataburzar Osimhen ba ta kare ba

A cewar dan jaridan:

"A cewar majiyata, Victor Osimhen ya amince da tayin albashin €350,000 daga Chelsea. Da farko ya nemi €500,000 amma Chelsea ta nemi ragi.

Kara karanta wannan

Atiku da Obi sun yi martani kan inyamura mai ikirarin kashe yan Najeriya a Canada

"Sai dai kuma, lokacin murna ga masoyan Chelsea bai yi ba, domin tataburzar ba ta kare ba. Kungiyoyin Saudiya na ci gaba da rige rigen cimma yarjejeniya da dan wasan."

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyar Napoli da Osimhen ke taka leda a yanzu ta amince da tayin Chelsea na mika mata dan wasan Najeriyan.

Osimhen ya karbi tayin Napoli

A wani labarin, mun ruwaito cewa dan wasan gaba na Nigeria, Victor Osimhen ya amince da tayin kungiyar kwallon kafa ta Napoli na €70m da kuma hasafin €10m.

Osimhen wanda ya saka kwallaye 18 a raga a cikin wasanni 32 a lokacin zamansa a Lille, zai sanya riga mai lamba 9 a Napoli a kwantiragin shekaru biyar da karba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.