Cristiano Ronaldo Zai Yi Ritaya Daga Buga Kwallon Kafa? CR7 Ya Bayyana Shirinsa

Cristiano Ronaldo Zai Yi Ritaya Daga Buga Kwallon Kafa? CR7 Ya Bayyana Shirinsa

  • Fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya, Cristiano Ronaldo ya ce zai ci gaba da taka leda duk da cewa shekarunsa sun kai 39
  • Cristiano Ronaldo ya kuma yi bayani kan shirinsa na yin ritaya daga buga kwallon kafa yayin da ya ke taka leda a kungiyar Al-Nassr
  • A yayin da rade-radi suka yi yawa kan cewa zai yi aikin koci bayan ritayarsa, Ronaldo ya ba ya tunanin akwai abincinsa a aikin koci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gabanin kocin Portugal, Roberto Martinez ya bayyana sunayen 'yan wasansa da za su fafata a gasar 'Nations League,' Cristiano Ronaldo ya bayyana shirinsa na yin ritaya daga kwallo.

Kara karanta wannan

"Zan tsaya da kafafuna": Dan takarar gwamnan PDP ya sha alwashi, ya bugi kirji

Tsohon dan wasan na Real Madrid ya ce har yanzu yana son ci gaba da bugawa kasarsa wasa amma idan lokacin ritayarsa ya zo, zai tabbata ya shirya.

Cristiano Ronaldo ya yi magana kan shirinsa na yin ritaya daga taka leda
Cristiano Ronaldo ya ce zai ci gaba da taka leda yayin da ya yi magana kan shirinsa na ritaya. Hoto: @Cristiano
Asali: Twitter

Haka kuma, tsohon dan wasan na Manchester United ya ce ba shi da ra'ayin aikin horar da 'yan wasa bayan ritayarsa, inji rahoton Forbes.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Cristiano ya ce

A zantawarsa da manema labarai, Cristiano Ronaldo wanda a yanzu ya ke taka leda a kungiyar kwallon kafar Saudiya ta Al-Nassr ya bayyana cewa:

"Idan lokacin ritaya ta ya zo, ba zan fadawa kowa ba, kuma zai zama wani hukunci da zan yanke shi a kashin kaina, amma zan tabbatar na yi tunani mai zurfi a kai.
"A yanzu abin da nake so shi ne in taimakawa tawagar kasata a wasannin da za su yi nan gaba. Muna da gasar 'Nations League' a gabanmu kuma ina son yin wasa a gasar."

Kara karanta wannan

Bruno Labbadia: Abubuwa 5 masu mahimmanci game da sabon kocin Super Eagles

Ronaldo zai zama koci?

Shafin Goal.com ya ruwaito Ronaldo ya yi karin haske kan rade-radin zai zama koci bayan ritayarsa.

"“A halin yanzu, ba na tunanin zama kocin wata kungiya. Babu tunanin hakan a zuciyata kwata kwata, kuma ba na tunanin zan iya yin aikin horarwa a rayuwata.
Sai dai ina da ra'ayi na yin wasu abubuwan daban da ba su shafi wasan kwallon kafa ba, amma Ubangiji ne kadai ya san abin da zai faru nan gaba."

- A cewar CR-7.

Ronaldo: Dan wasa mafi albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, ya samu albashin dala miliyan 260 a cikin watanni 12 kacal.

Wannan ya sa Ronaldo ya zamo dan wasa mafi karbar albashi a duniya bayan kwantiraginsa da kungiyar A-Nassr da ta sama masa dala miliyan 200 a kaka daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.