Bruno Labbadia: Abubuwa 5 Masu Mahimmanci Game da Sabon Kocin Super Eagles

Bruno Labbadia: Abubuwa 5 Masu Mahimmanci Game da Sabon Kocin Super Eagles

Abuja - Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF), ta sanar da cewa ta cimma yarjejeniya da wani dan kasar Jamus, Bruno Labbadia, domin ya zama babban kocin kungiyar Super Eagles.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Mai ba da horon mai shekaru 58, wanda ya kware sosai a harkar kwallon kafa ta Jamus, zai fara aikin horar da ‘yan wasa a wajen kasarsa da Najeriya.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon kocin Super Eagles.
Hukumar kwallon kafar Najeriya ta nada Bruno Labbadia sabon kocin Super Eagles. Hoto: Marco Steinbrenner/Getty, @thenff/X
Asali: Getty Images

A cewar sanarwar da NFF ta fitar shafinta na X, wannan nadin na Bruno Labbadia zai fara aiki nan take.

tsohon kocin Bayer Leverkusen zai jagoranci Super Eagles a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika (AFCON) na 2025 mai zuwa.

Kara karanta wannan

NFF ta nada sabon kocin Super Eagles daga Turai da dan kasa ya yi murabus

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Super Eagles za ta kara da Jamhuriyar Benin da kuma Amavubi ta Rwanda a wasannin neman cancantar shiga gasar AFCON din.

A yayin da ake ci gaba da yin tsokaci kan nadin tsohon kocin Jamus, Legit Hausa ta yi karin haske kan muhimman bayanai da za a sani game da sabon manajan Super Eagles.

Muhimman abubuwa a kan Labbadia

Kwararren dan wasan gaba

Sabon kocin Super Eagles ya yi kaurin suna a lokacin da yake taka leda tare da kungiyoyi da dama a matakai daban-daban na kwallon kafa ta Jamus.

Labbadia, wanda ya kwashe kusan shekaru ashirin ya na taka leda, ya zura kwallaye sama da 250.

A matsayinsa na dan wasan gaba, ya taka leda a fitattun kungiyoyi da suka hada da Werder Bremen da Bayern Munich, inda ya samu nasarar lashe kofin Bundesliga.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Dan takarar gwamna ya shiga tashin hankali, 'yan bindiga na farautarsa

Aikin horar da 'yan wasa

Tun lokacin da ya fara aikin horarwa a 2003 tare da Darmstadt 98, tsohon manajan ya nuna kwarewara da kuma saurin sabawa da 'yan wasa a duk kungiyar da ya jagoranta.

Yayin da bayanai daga shafin Sofascore ke nuna fifikon sa a kan tsarin wasa na 4-2-3-1, aikinsa na horarwa yana nuna karfin sha'awarsa ga ba 'yan wasa damar nuna bajintarsu.

Nasararsa a aikin horarwa

A tsawon shekaru goma da ya yi yana horar da ‘yan wasa, Koci Labbadia ya jagoranci wasu manyan kungiyoyi a gasar Bundesliga ta Jamus.

Kocin mai shekaru 58 ya karbi ragamar horar da Bayer Leverkusen, Hamburger SV, da VfL Wolfsburg. Sai dai Labbadia bai sami damar daga wani kofi ba a tarihin aikinsa.

Nasararsa da kawai ya samu ita ce jagorantar VfB Stuttgart a kakar 2011/12 zuwa gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa, bisa ga bayanai daga FotMob.

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Dattawan Arewa sun yi martani kan lamarin, sun tura sako ga Sultan

Kwararren mai ceton kungiya

Wani muhimmin batu da ya kamata masu son tawagar 'yan wasan Najeriya su sani game da sabon kocin shine laƙabin da ya samu na, 'Kwararren mai ceton kungiyoyi'.

Koci Labbadia ya yi kaurin suna a matsayin daya daga cikin manyan manajojin da ake neman taimakonsu a duk lokacin da kungiya ke fuskantar barazanar durkushewa.

Labbadia na iya amfani da kwarewarsa a kan Super Eagles, musamman yadda kungiyar ta samu kanta a kasan teburi na rukunin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA.

Ya fito daga tsatson Italiya

Sabon kocin Super Eagles ya na alfahari da kasancewar dan tsatson Italiya. Tushen dangin Labbadia ya samo asali ne daga Lenola, wani gari a yankin Lazio na Italiya.

Iyayensa na Italiya sun koma Jamus a matsayin Gastarbeiter kuma suka zauna a Schneppenhausen, kusa da Darmstadt.

NFF: An nada sabon kocin Super Eagles

A wani rahoton kuma, Legit Hausa ta bayyana cewa hukumar kwallon kafar Najeriya ta nada Bruno Labbadia a matsayin sabon kocin Super Eagles.

Ana sa ran gogaggen mai ba da horon zai jagoranci tawagar Najeriya a wasannin neman gurbin shiga gasar AFCON ta 2025 mai zuwa a watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.