Gasar kofin kwallon kafa ta duniya: Najeriya zata kara da kasashen Argentina, Crotia, da Iceland, a rukunin D
Najeriya zata kara da kungiyar kwallon kafa ta kasar Argentina a karo na biyar a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa da za a buga a kasar Rasha shekara mai zuwa.
A baya Najeriya ta taba kwafsawa a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da kasar Argentina a shekarun 1994, 2002, 2010, da 2014 ba tare da ko sau daya Najeriya ta taba yin nasara ba.
Wannan haduwa na iya zama tamkar dama ga Najeriya ta fara daukan fansa a kan galabar da kasar Argentina tayi a kan ta a shekarun baya.
A yau ne dai hukumar kula kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta raba dukkan kasashen da suka yi nasarar fitowa buga gasar zuwa rukunai takwas mai dauke da kasashe hudu a kowanne rukuni da zasu fafata domin neman zuwa zagaye na gaba.
DUBA WANNAN: Har yanzu ba a kamo ni a aiyukan raya kasa ba - Jonathan ya kalubanci gwamnatin Buhari
Najeriya ta fada a rukunin D mai dauke da kasashen Argentina, Crotia, da Iceland. Kasashe 32 ne zasu fafata neman nasarar daukan kofin na duniya.
Za a buga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya shekara mai kamawa a kasar Rasha.
Yayin rarraba kasashen ya zuwa rukunan da zasu kwafsa, tsofin shahararrun 'yan wasan kwallon kafa sun halarci wurin rabon. Daga cikin su akwai Maradona, Pele, Kanu, Okocha, Seedorf, Infantino, Ronaldinho, da sauran su.
Hakazalika shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya halarci wurin taron kuma har ma ya yi jawabi ga mahalarta taron.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng