NFF Ta Nada Sabon Kocin Super Eagles Daga Turai da Dan Kasa Ya Yi Murabus

NFF Ta Nada Sabon Kocin Super Eagles Daga Turai da Dan Kasa Ya Yi Murabus

  • Hukumar NFF a Najeriya ta tabbatar da nadin sabon kocin Super Eagles daga kasar Jamus mai suna Bruno Labbadia domin jagorantar tawagar
  • Nadin Labbadia na zuwa ne bayan murabus din tsohon dan kwallon kafar Najeriya, Finidi George a watan Yunin 2024 da ta gabata
  • NFF ta ce ta kammala yarjejeniya da sabon kocin tawagar Super Eagles na 37 a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Talata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta amince da nadin sabon kocin Super Eagles daga kasar Jamus, Bruno Labbadia.

Hukumar ta ce ta kammala yarjejeniya da Labbadia wanda shi ne kocin tawagar Super Eagles na 37 a tarihi bayan murabus din Finidi George.

Kara karanta wannan

Yusuf Bichi ya yi murabus: Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar DSS

NFF ta nada sabon kocin Super Eagles
Hukumar NFF ta nada sabon kocin Supr Eagles dan kasar Jamus, Bruno Labbadia. Hoto: @thenff.
Asali: Twitter

NFF ta nada sabon kocin Super Eagles

NFF ta bayyana haka ne da safiyar yau Talata 27 ga watan Agustan 2024 a shafinta na X inda ta ce nadin zai fara aiki nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Labbadia shi ne zai maye gurbin tsohon kocin Super Eagles, Finidi George da ya yi murabus a watan Yunin 2024 yayin da ake shirin nada sabon koci.

Finidi wanda tsohon kocin kwallaon kafa ta Enyimba ne ya karbi ragamar jagorantar tawagar a watan Afrilun 2024.

Tsohon kocin ya shafe watanni biyu ne kacal kafin ya yi murabus inda ya jagoranci wasanni biyu a kungiyar.

Wasu kungiyoyin kwallon kafa Labbadia ya jagoranta?

Sabon kocin, Labbadia tsohon dan wasa ne da ya taka rawa a Kaiserslautern da Bayern Munich da Darmstadt da Hamburger da Koln da Weder Bremen da sauransu.

Kara karanta wannan

Digiri dan Kwatano: Gwamnati ta lissafa jami'o'in Benin, Togo da ta amince da su

Daga bisani ya shiga harkar koci inda ya fara da Darmstadt da Greuther Furth da Bayer Leverkusen da Hamburger da Hertha Berlin da kuma Wolfsburg.

Super Eagles: Finidi George ya yi murabus

Kun ji cewa mun samu rahoton cewa kocin kungiyar Super Eagles, Finidi George ya yi murabus daga mukaminsa na jagorantar tawagar a Najeriya.

Murabus din bai rasa nasa da rashin tabuka wani abu bayan karbar ragamar Super Eagles da Finidi ya yi inda ake hasashen nada sabon koci daga Turai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.