Ana Tsaka da Neman Gurbi a Kofin Duniya, Kocin Super Eagles, Finidi Ya Yi Murabus

Ana Tsaka da Neman Gurbi a Kofin Duniya, Kocin Super Eagles, Finidi Ya Yi Murabus

  • Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa kocin Super Eagles, Finidi George ya yi murabus daga mukaminsa
  • Finidi mai shekaru 53 ya yi murabus ne a yau Asabar 15 ga watan Yuni makwanni kadan bayan karbar ragamar kungiyar
  • Hakan bai rasa nasaba da rashin katabus a wasanni biyu na neman gurbin gasar kofin duniya da aka yi a kwanakin nan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An ruwaito cewa kocin kungiyar Super Eagles, Finidi George ya yi murabus daga mukaminsa.

Murabus din bai rasa nasa da rashin tabuka wani abu bayan karbar ragamar Super Eagles da Finidi ya yi.

Finidi George ya yi murabus daga kocin Super Eagles
Bayan rashin katabus, kocin Super Eagles, Finidi Geroge ya yi murabus. Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP.
Asali: Getty Images

Super Eagles: Finidi George ya yi murabus

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Sanusi II ya fadi kokarin Abba Kabir bayan barnar da Ganduje ya tafka

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da dan jarida a bangaren wasanni, Adepoju Tobi Samuel ya walllafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Majiyoyina sun tabbatar min cewa Finidi George ya yi murabus daga mukaminsa na kocin Super Eagles."

- Tobi Samuel

Wani dan jarida a bangaren wasanni, Sulaiman Pooka Adebayo shi ma ya tabbatar da haka.

"Finidi George ya yi murabus bayan mayar da shi baya yayin da za a dauko koci daga kasar waje."

- Sulaiman Pooja

Finidi George ya karbi ragamar Super Eagles

Finidi George mai shekaru 53 ya karbi ragamar kocin kungiyar ne bayan karewar kwantiragin tsohon kocinta, Jose Peseiro a watan Faburairun 2024.

Ya kasance a matsayin mataimakin Peseiro na tsawon watanni 20 kafin kwantiragin tsohon kocin ya kare.

Murabus din bai rasa nasaba da rashin katabus yayin da Super Eagles ta yi rashin nasara a wasanni uku a neman gurbin gasar kofin duniya.

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashin da ya sace dabbobi, ya kalmashe kudin mutane a aljihu

Super Eagles za ta dauko sabon koci

Kun ji cewa Hukumar kula da kwallon kafar Najeriya (NFF) ta yanke shawarar dauko hayar mai horar da 'yan wasa daga Turai domin jan ragamar tawagar Super Eagles.

An ce NFF za ta dauko wa Super Eagles hayar koci daga Turai biyo bayan shan kashin da tawagar ta yi a wasanni biyu jere, karkashin Finidi George.

Kwamitin zartarwar hukumar sun yanke wannan shawarar ne a wani taro da suka yi a makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel