Messi Ya Magantu Kan Ritaya Daga Kwallon Kafa, Ya Fadi Kungiyarsa Ta Ƙarshe

Messi Ya Magantu Kan Ritaya Daga Kwallon Kafa, Ya Fadi Kungiyarsa Ta Ƙarshe

  • Lionel Messi ya magantu kan kungiyar kwallon kafa da zai yi ritaya bayan shahara da ya yi a fagen buga tamola
  • Messi ya tabbatar da cewa kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami ita za ta kasance kungiyarsa ta karshe a kwallon kafa
  • Fitaccen ɗan wasan kwallon mai shekaru 36 ya bayyana haka ne a jiya Laraba 12 ga watan Yuni yayin hira da 'yan jarida

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Miami, Amurka - Fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa a duniya, Lionel Messi ya bayyana kungiyar da zai ajiye tamola.

Messi ya ce zai yi ritaya ne a kungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami da ke buga gasar 'Major League Soccer' a kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Jigon APC, Salihu Lukman ya nakasa jamiyyar bayan ya yi murabus, ya jero dalillai

Messi ya bayyana kungiyar da zai yi ritaya a kwallon kafa
Lionel Messi zai yi ritaya a kungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami. Hoto: Pau Barrena.
Asali: Getty Images

Messi ya magantu kan ritaya a kwallo

Fitaccen ɗan wasan mai shekaru 36 ya bayyana haka ne yayin hira da ESPN a jiya Laraba 12 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina tunanin Inter Miami za ta zamo kungiyar ƙwallon ƙafa ta karshe da zan buga wasa."
"Na shafe shekaru ina buga wasa, ina kaunar buga kwallon kafa, ina jin dadin harkar kwallon kafa."
"Amma abin takaici ne duka wannan zai zo karshe, abu ne mai matukar wahala barin Nahiyar Turai zuwa nan Miami."

- Lionel Messi

Kungiyoyin da Messi ya bugawa ƙwallo

Tun bayan bayyanarsa a fagen kwallon kafa a 2004, Messi ya buga kwallo ne a ƙungiyoyin kwallon kafa uku kadai a rayuwarsa.

Kungiyoyin sun hada da Barcelona da ke Sifen da PSG a kasar Faransa da kuma Inter Miami da ke Amurka.

Kara karanta wannan

"Yan bindiga sun shiga uku," Gwamna ya sha alwashin dawo da zaman lafiya duk runtsi

Ɗan wasan ya fi shahara a kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona inda a nan ne ya yi fice tare da kafa tarihi a duniya.

Mbappe ya koma kungiyar Real Madrid

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen dan wasan gaba na France, Kylian Mbappe ya koma Real Madrid da buga wasa.

'Dan wasan ya sanya hannu a duka takardun yarjejeniya da kungiyar domin fara wasa a sabuwar kaka mai zuwa.

Madrid ta dade tana zawarcin dan wasan shekaru da dama kafin samun nasarar dauke shi daga kungiyar PSG.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.