Fitaccen Ɗan Kwallo, Mbappe Ya Sanar da Barin PSG a Bidiyo Mai Sosa Zuciya
- Ɗan wasan gaba ɗan asalin ƙasar Faransa, Kylian Mbappe ya tabbatar da cewa zai bar ƙungiyar kwallon ƙafa ta PSG a karshen kakar wasa ta bana
- Fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa mai kimanin shekaru 25 ya ce zai buga wa PSG wasan ƙarshe a gida ranar Lahadi, 12 ga watan Mayu
- Mbappe ya bayyana cewa ba zai tsawaita kwantiraginsa a PSG ba kuma zamansa a ƙungiyara zai kare nan da makonni ƙalilan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Paris, France - Fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa, Kylian Mbappe, ya sanar da barin ƙungiyar Paris Saint-Germain watau PSG a karshen kakar wasa ta bana 2023/2024.
Mbappe ya bayyana cewa zamansa ya zo ƙarshe a PSG a wani faifan bidiyo da ya bazau a kafafen sada zumunta ranar Jumu'a, 10 ga watan Mayu.
Mbappe ya tabbatar da barin PSG
Babban ɗan wasan mai buga tamaula a gaba ya tabbatar da zai bar PSG a bidiyon da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabin da ya yi, Mbappe ya ce:
"Ina son faɗa maku kuma dama na ce zai gaya muku komai idan lokaci ya yi, to yanzu ina son sanar da ku cewa wannan ce shekarata ta karshe a PSG, ba zan tsawaita zamana ba.
"Zan buga wasan gida na ƙarshe a filin ƙwallon Parc des Princes ranar Lahadi. Shekaru da dama sun shuɗe, a nan ne na samu damar zama ɗan wasan ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka yi fice a duniya.
"Na zo nan, na ƙara gogewa a wannan ƙungiya kuma na haɗu da manyan zakarun kwallon ƙafa, waɗanda tarihi ba zai manta da su ba, na ƙara girma da samun kwarewa duk da nasara da kuskuren da na taɓa yi."
Legit.ng ta tattaro cewa wasu rahotanni sun yi iƙirarin cewa tuni Mbappe ya cimma yarjejeniya da ƙungiyar kwallon ƙafa ta Real Madrid.
Real Madrid ta lashe kofin La liga
A wani rahoton kuma Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fitar da abokan hamayyarta na Sifaniya daga gasar La Liga bayan da ta lashe kofin a ranar Asabar
Real Madrid ta lashe kofin na La Liga karo na 36 bayan doke Cadiz da ci 3-0 yayin da Barcelona ta sha kashi a hannun Girona da ci 4-2.
Asali: Legit.ng