"Ba Irinku Ba Ne": EFCC Ta Tura Sako Ga Shugabanni Game da Halayen Yar'adua
- Yayin da ake bikin tunawa da marigayi, Umaru Musa Yar'adua, shugaban hukumar EFCC ya yabawa tsohon shugaban kasar
- Ola Olukoyede ya ce inama ace shugabannin Najeriya suna koyi da irin halin gaskiya da dattaku na marigayin lokacin da ya ke mulki
- Shugaban hukumar ya bayyana haka a jiya Litinin 6 ga watan Mayu yayin taron tunawa da marigayin bayan cika shekaru 14 da rasuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya magantu kan halayen marigayi Umaru Musa Yar'adua.
Olu Olukoyede ya ce inama ace shugabannin Najeriya za su yi koyi da halayen marigayin yayin da ke raye.
EFCC ta yabawa halin Yar'adua
Shugaban EFCC ya bayyana haka yayin taron tunawa da marigayin a jiya Litinin 6 ga watan Mayu wanda hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Yar'adua ya nuna halin dattaku da gaskiya da kuma nagarta a lokacin mulkinsa daga 2007 zuwa 2010.
Daraktan hulda da jama'a na hukumar, Mista Wilson Uwujaren ya wakilci Olukoyede a taron inda ya yabawa salon mulkin Yar'adua.
EFCC ta fadi matsalar Najeriya
"Hukumar EFCC ta yaba da halayen kirki da gaskiya da Yar'adua ya nuna, wannan shi ne matsayarta wato gaskiya da rikon amana."
"Babban makasudin wannan taro shi ne gaskiya da shugabanci nagari wanda abin da ya rike kenan lokacin daya ke gwmanan Katsina da kuma shugaban Najeriya."
"Idan ana magana kan tashin farashin kaya da cin hanci da wasu matsaloli a kasar, duk rashin gaskiya ke jawo su, ya kamata mu yi koyi da halayen kirki a dukkan abin da muke yi."
- Ola Olukoyede
Gowon ya yabawa mulkin Yar'adua
A wani labarin, an ji yadda tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya yabawa salon mukin marigayi Umaru Musa Yar'adua a Najeriya.
Gowon ya ce Yar'adua mutum ne mai gaskiya wanda bai saci ko da kwabon al'umma ba inda ya ce ya so gyara Najeriya.
Wannan na zuwa ne yayin da ake bikin tunawa da Yar'adua bayan cika shekaru 14 da rasuwa a ranar 5 ga watan Mayun 2010.
Asali: Legit.ng