Ahmed Musa da Wani Ɗan Wasa Zasu Kafa Muhimmin Tarihi 1 Idan Najeriya Ta Lashe Kofin AFCON

Ahmed Musa da Wani Ɗan Wasa Zasu Kafa Muhimmin Tarihi 1 Idan Najeriya Ta Lashe Kofin AFCON

  • Tawagar Super Eagles ta Najeriya na fatan lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) karo na huɗu a tarihi
  • Yayin da Najeriya ke shirin karawa da masu masaukin baƙi a wasan karshe ranar Lahadi, ƴan wasa biyu zasu kafa tarihi idan Super Eagles ta yi nasara
  • Kaftin Ahmed Musa da ɗan wasan tsakiya, Kenneth Omeruo, zasu zama ƴan wasan Najeriya na farko da zasu lashe kofin sama da sau ɗaya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tawagar ƴan wasan Najeriya Super Eagles za su ɓarje gumi da ƴan wasan Cote d'Ivoire a wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON).

Za a fafata wannan wasa ne domin tantance zakara a gasar bana ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu, 2024 da misalin ƙarfe 9:00 na dare agogon Najeriya.

Kara karanta wannan

AFCPN 2023: Kocin Cote d'Ivoire ya fadi hanyar da za su bi don doke Najeriya a wasan karshe

Ahmed Musa da Omerou.
Ahmed Musa da Wani Ɗan Wasa Daya da Zasu Kafa Tarihi Idan Najeriya Ta Ci Kofin AFCON Hoto: Ahmed Musa, Kenneth Omeruo
Asali: Twitter

Ƴan wasan Najeriya biyu, kaftin din Super Eagles, Ahmed Musa da ɗan wasan tsakiya, Kenneth Omeruo, zasu kafa tarihin idan har suka lashe gasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan har Najeriya ta lashe gasar ranar Lahadi, Ahmed Musa da Omeruo zasu zama ƴan ƙwallon kasar nan na farko da suka jijjiga kofin AFCON sau biyu a tarihi.

Musa da Omeruo suna ɗaya daga cikin ƴan wasan Super Eagles da suka lashe kofin nahiyar Afirka a 2013 karkashin mai horaswa marigayi Stephen Keshi, The Nation ta tattaro.

Yadda Najeriya ta lashe kofin AFCON 2023

Najeriya ta doke abokiyar hamayyarta Afirka ta Kudu a wasan kusa da na karshe na gasar AFCON 2023 inda ta samu tikitin zuwa wasan karshe.

Wasan dai an tashi 1-1 bayan mintuna 90 tsakanin Super Eagles da Bafana Bafana, aka zarce ƙarin lokaci ba tare da ƙara jefa kwallo ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai lula zuwa kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka AFCON? Gaskiya ta bayyana

Daga nan aka yi bugun daga kai sai mai tsaron raga wanda Najeriya ta doke Afirka ta kudu da ci 4-2.

A cikin wasan, Super Eagles ta Najeriya da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu sun zura kwallaye ɗai-ɗai ne daga bugun fenariti.

Tinubu zai je kallon wasan ƙarshe

A wani rahoton na daban Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai je kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin AFCON wanda tawagar Super Eagles zata kara da Ivory Coast.

Ƴan wasan Najeriya na shirye-shiryen ɓarje gumi da masu masaukin baƙi ƙasar Ivory Coast a wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262