AFCON: Ganduje Ya Bi Sahun Kwankwaso Inda Ya Tura Sako Ga Tawagar Super Eagles, Bayanai Sun Fito
- Shugaban jam’iyyar APC, Dakta Umar Ganduje ya roki addu'a ga Najeriya don samun nasara a wasansu da Angola
- Ganduje ya nuna goyon bayan ne tare da neman addu’a ga kungiyar ta Super Eagles a karawar da za su yi a gobe Juma’a
- Umar ya yi wannan kira ne a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu yayin tarbar kwamitin gasar matasa ta APC
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Yayin da ake ci gaba da gasar cin kofin AFCON a Ivory Coast, shugaban APC, Umar Ganduje ya nuna goyon baya ga tawagar Najeriya.
Ganduje ya nuna goyon bayan ne tare da neman addu’a ga kungiyar ta Super Eagles a karawar da za su yi da kasar Angola.
Yaushe Najeriya za ta yi wasa da Angola?
Kungiyar ta samu hayewa zagayen kwata fainal bayan doke kasar Kamaru da ci kwallo biyu da nema, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani an hada su da kasar Angola wanda za su buga wasa a gobe Juma’a 2 ga watan Faburairu.
Shugaban jam’iyyar ya yi wannan kira ne a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu yayin tarbar kwamitin gasar matasa ta APC.
Yayin da ya ke nuna kwarin gwiwarsa kan nasarar Super Eagles, Ganduje ya ce ya na bibiyar nasarorin da suke samu.
Ya ce ya na da tabbacin cewa kungiyar ta Najeriya za ta iya cin kofin da ake bugawa a kasar Ivory Coast.
Martanin Ganduje kan wasan Najeriya
Ya ce:
“Kamar yadda nake Patron na kungiyar kwallon kafa ta matasa, ina kallon dukkan wasannin gasar AFCON da ake bugawa.
“Zan iya fadan wadanda suke cikin kungiyar da kuma sanar da ku cewa a gobe Najeriya za ta buga da kasar Angola.
“Mun sani cewa muna da masu tsaron baya da kyau saboda kwallo daya kawai aka sha mu, haka gaban mu ma su na da kyau.”
Ganduje ya roki ‘yan Najeriya su taya Najeriya da addu’a don samun nasara a wasansu da Angola, cewar Leadership.
Ya kara da cewa:
“Zamu ci gaba da addu’a saboda Najeriya ta samu nasara a wasanta da Angola kuma za mu je matakin kusa da na karshe.”
Kwankwaso ya taya Najeriya murna
Kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwasa ya taya tawagar kwallon kafar Najeriya murnar hayewa zagayen gaba.
Kwankwaso ya bayyana haka ne bayan Najeriya ta samu damar hayewa zuwa matakin gaba daga rukuni.
Asali: Legit.ng