AFCON 2023: An Fadi Makudan Kudin da Najeriya Za Ta Samu Idan Ta Doke Angola
- Wani rahoto da ke fitowa ya tabbatar da cewa Najeriya za ta samu kuɗi masu tsoka idan ta doke Angola a wasan daf da na kusa da na ƙarshe
- A cikin jadawalin da hukumar ƙwallon kafa ta Afrika (CAF) ta fitar, Super Eagles za ta samu tukuicin $2.5m (N2.24bn) idan ta tsallake zuwa wasan kusa da na ƙarshe
- Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa Super Eagles sun riga sun samu kudi $800,000 a matakin rukuni da $1.2m a zagaye na 16
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta kara da Palancas Negras na Angola domin samun gurbi a wasan daf da na ƙarshe a gasar cin kofin nahiyar Afirika karo na 34 a ƙasar Cote d'Ivoire.
Akwai tukuicin $2.5m (kimanin N2.24bn) ga waɗanda suka yi nasara, tukuicin da CAF ta ware domin duk tawagar da ta yi nasara a zagayen daf da na kusa da na ƙarshe.
Super Eagles dai tuni sun samu $800k a a matakin rukuni da kuma $1.3m a zagaye na 16 da suka yi nasara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Samun nasarar a kan Angola a wasan da za a yi zai tabbatar da cewa Super Eagles ta samu tukuicin $2.5m, cewar rahoton Goal.com.
Tarihin karawar Najeriya da Angola
Wannan wasan yana da muhimmanci fiye da batun samun tukuicin kuɗi da samun gurbi a matakin wasan kusa da na ƙarshe.
Ga ƴan wasa da magoya bayan Najeriya, wasan wata dama ce ta ɗaukar fansa.
Har yanzu ba a manta da rawar da Angola ta taka wajen daƙile yunƙurin Najeriya na zuwa gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarar 2006 ba.
A lokacin dai Super Eagles ta yi kasa a gwiwa bayan ta sha kashi da ci 1-0 a Luanda, sannan aka tashi kunnen doki 1-1 a Kano.
Nawa za a ba ƙungiyar da ta lashe AFCON 2023?
Yayin da babbar kyautar $7m ga wanda ya lashe gasar AFCON da $4m ga wanda ya zo na biyu abu ne mai ban sha'awa, Super Eagles na ci gaba da mai da hankali kan ƙalubalen da ke a gabansu.
A cewar Soccernet.ng, Najeriya za ta kara da Angola a filin wasa na Stade Félix Houphouët-Boigny da ke Abidjan a ranar Juma'a 2 ga watan Fabrairu.
Yayin da Palancas Negras ke burin buga wasansu na farko a wasan kusa da na ƙarshe, Najeriya na da tarihin kai wa matakin kusa da na ƙarshe a wasanni 15 cikin 19 da ta buga a baya a gasar.
Kwankwaso Ya Taya Super Eagles Murna
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya ƙungiyar Super Eagles murnar kai wa ga zagage na 16 a gasar cin kofin AFCON.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya ce kokarin da ƙungiyar Super Eagles ta yi na zuwa zagaye na gaba abin a yaba ne matuƙa.
Asali: Legit.ng