Christiano Ronaldo Ya Ce Babu Sauran Adawa Tsakaninsa Da Messi

Christiano Ronaldo Ya Ce Babu Sauran Adawa Tsakaninsa Da Messi

  • Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa Christiano Ronaldo ya ce babu wata adawa tsakaninsa da Messi
  • Ronaldo ya bayyana cewa kowanensu ya taka leda yadda ya kamata kuma yanzu duk suna buga ƙwallo a wajen Turai
  • Ronaldo ya ce wasu daga cikin masoyansu ne ke ganin kamar babu wata kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da Messi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan na AlNassr FC, kuma ɗan asalin ƙasar Portugal, Christiano Ronaldo, ya ce adawarsa da Lionel Messi ɗan ƙasar Argentina ta ƙare.

Ronaldo ya ce ba dole ba ne a ce duk wani masoyinsa sai ya ƙi jinin Messi, hakan nan suma masoyan na Messi ba dole ba ne sai sun ki jinin Ronaldo kamar yadda Marca ta wallafa.

Ronaldo ya ce adawar da ke tsakaninsa da Messi ta zo ƙarshe
Ronaldo ya ce babu adawa a tsakaninsa da Messi. Hoto: @brfootball, @AlNassrFC_EN
Asali: Twitter

Ronaldo ya ce yanzu babu buƙatar yin adawa da Messi

Kara karanta wannan

NYSC Ta Magantu Kan Sace Masu Yi Wa Kasa Hidima, Ta Bayyana Babban Kuskure 1 Da Suka Tafka

Ronaldo ya bayyana cewa a tsawon shekarun da suka kwashe su a bugawa manyan kulob-kulob wasa, da yawa daga cikin masoyansu na gaba da kowane ɗaya daga cikinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce babu buƙatar kiyayyar da masoyan kowanne ke yi wa kowane ɗaya daga cikinsu domin kuwa sun yi tashe a duniya, kuma ana mutuntasu a ko'ina.

Ronaldo ya ƙara da cewa Messi ya taka ledarsa yadda ya kamata a yayinda shima ya taka ta sa har ta kai ga yanzu haka duk ba sa buga ƙwallo a Nahiyar Turai.

Asalin adawar da ke tsakanin Ronaldo da Messi

Ronaldo ya kuma ƙara da cewa sun shafe sama da shekaru 15 suna buga wasa a tare duk da dai kowa da kulob ɗin da yake bugawa wasa kamar yadda NBC Sports ta wallafa.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Bayin Allah Da Sace Mutane Masu Yawa

Sunan Christiano Ronaldo dai ya ƙara fitowa fili ne a lokacin da yake bugawa Real Madrid wasa, a yayinda shi kuma Messi sunansa ya fito a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

Asalin adawar da ke tsakanin mabiya manyan 'yan wasan biyu ta samo asali ne daga tashen da suka yi a lokaci daya, kuma a manyan ƙungiyoyin kwallo na duniya.

Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Ronaldo da Lionel Messi, sai dai magoya bayansu ne suka dauki abin da zafi har suke ganin kamar akwai wata adawa tsakanin gwanayen biyu.

Messi ya dara Ronaldo shahara ta bangaren cin kofi

Legit.ng a baya ta kawo wani rahoto na kundin bajinta na Guiness, inda aka bayyana cewa Lionel Messi ya fi Christiano Ronaldo cin kofi a shekarun da suka shafe suna taka leda.

Rahoton ma Guiness ya bayyana cewa Messi ya ci kyautar kofuna 41 ne, a yayinda Ronaldo kuma yake da guda 40.

Kara karanta wannan

Abin Mamaki: Wata Akuya Ta Haifi Rabi Mutum Rabi Akuya a Wata Jihar Arewa, Bidiyonta Ya Yadu

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng