Jam'iyyar AA Ta Taso Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai a Gaba, Tana Neman Kwace Kujerarsa

Jam'iyyar AA Ta Taso Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai a Gaba, Tana Neman Kwace Kujerarsa

  • Jam'iyyar Action Alliance (AA) na neman kotun saurararon ƙararrakin zaɓe da ta da soke zaɓen mataimakin kakakin majalisar wakilai
  • Jam'iyyar ta kafa hujja da cire sunanta da tambarinta da aka yi a takaradar kaɗa kuri'a a zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairu
  • Sai dai, shaidan jam'iyyar APC ya bayyana cewa wanda ya shigar da bai cancanci yin takara ba kwata-kwata a zaɓen

Jihar Abia - Jam'iyyar Action Alliance (AA) a jihar Abia ta buƙaci kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya mai zamanta a birnin Umuahia, ta soke zaɓen mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jam'iyyar dai ta gabatar da buƙatar ta ne bisa zargin cewa an cire sunanta da tambarinta daga cikin takardar kaɗa ƙuri' a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Tsohon Gwamna Zai Maye Gurbin Omisore a Kujerar Sakataren Jam'iyyar Na Kasa? Bayanai Sun Fito

Jam'iyyar AA na neman a soke zaben Benjamin Kalu
Jam'iyyar AA ta bukaci kotu ta soke zaben Benjamin Kalu Hoto: @OfficialBenKalu
Asali: Twitter

Mohammed Ndalahi, lauyan ɗan takarar jam'iyyar AA a zaɓen, Ifeanyi Igbokwe, shi ne ya shigar da wannan buƙatar a zaman kotun na ranar Asabar.

Mai shigar da ƙarar bai cancanci tsayawa takara ba, shaidan Kalu da APC

Da yake magana lokacin da Mr Ndalahi yake masa tambayoyi, shaidan jam'iyyar APC da Benjamin Kalu, Cyril Kwubiri, ya yi zargin cewa jam'iyyar AA ba ita bace ta tsayar da Mr Igbokwe takara ba, sannan bai yi takara ba a zaɓen.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai, Mr Kwubiri, ya amsa cewa babu ko ɗaya daga cikin takardun da ya gabatar domin nuna cewa ba a tsayar da Igbokwe takara ba bisa ƙa'ida da suka fito daga wajen jam'iyyar APC.

Kotun mai alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Samson Gang, ta ɗage zaman sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga watan Agusta domin karɓar rubutattun bayanan ƙarshe na ɓangarorin biyu, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamnan PDP Ya Sake Nada Kwamishinonin Magabacinsa

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Akwa Ibom, Uno Eno, ya sake naɗa dukkanin kwamishinonin tsohon gwamna Emmanuel, a matsayin kwamishinoninsa.

Gwamnan ya bayyana cewa ya yi hakan ne domin saka musu na wucin gadi kan gudunmawar da suka ba shi lokacin yaƙin neman zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel