Sanatoci 3 da Hukumar EFCC ke Nema Sun Zama ‘Yan Gaba a Takarar Majalisar Dattawa

Sanatoci 3 da Hukumar EFCC ke Nema Sun Zama ‘Yan Gaba a Takarar Majalisar Dattawa

  • Bukola Saraki ya zama shugaban majalisa a 2015, amma a karshe ya kare da rikici da EFCC da CCT
  • Wannan karo jam’iyyar APC ta ayyana Godswill Akpabio wanda EFCC ta taba yin bincike a kan shi
  • EFCC ta taba tsare Abdulaziz Yari, shi kuwa Orji Uzor Kalu har gidan yari ya shiga saboda zargin sata

Abuja - Rahoton nan ya tattaro jerin masu burin zama shugabannin majalisar dattawa da kuma tarihin bincikensu da hukumar EFCC ta taba yi a baya.

1. Godswill Akpabio

Tsohon Gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio shi ne wanda jam’iyyar APC ta fifita a takarar majalisa, duk da ana zargin akwai kashi a jikinsa.

A wani dogon rahoto da Premium Times ta fitar, ta ce ana tuhumar Sanata Godswill Akpabio da rashin gaskiya bayan shekaru takwas da ya yi a Gwamna.

Kara karanta wannan

Barazanar Sanatocin Jihohin Arewa Ya Jawo APC Ta Ji Uwar Bari a Kan Takarar Majalisa

Akwai lokacin da aka tasa hukumar EFCC a gaba ta binciki Akpabio a kan zargin satar N108bn. Wannan bai hana shi zama Minista da ya shigo APC ba.

Sanatoci
Abdulaziz Yari, Uzor Kalu da Godswill Akpabio Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. Orji Uzor Kalu

Shi kuwa Sanata Orji Uzor Kalu sai da ya shiga gidan yari bayan kotu ta same shi da laifin taba baitul-malin jihar Abia, aka yanke masa daurin shekaru 12.

Daga baya ne kotun koli ta fito da tsohon Gwamnan na Abia, ta kuma bukaci a sake yin shari’a da shi. Har yanzu ba a soma shari’ar Kalu da hukumar EFCC ba.

Duk da cewa tun 2007 jami’an EFCC su ke hawa sama da kasa da Kalu, Sanatan Abia ta Arewa ne shugaban masu tsawatarwa, yanzu yana harin shugabanci.

3. Abdulaziz Yari

Na karshe a jerin shi ne tsohon Gwamna a jihar Zamfara, Abdulaziz Yari wanda ya fara lashe zaben majalisa a 2019, amma kotu ta hana a rantsar da su.

Kara karanta wannan

Yari da Wasu Fusatattun Sanatoci 3 Masu Neman Shugabancin Majalisa Sun Yi Kus-Kus da Shugabannin APC

Jaridar ta ce Alhaji Yari ya sha bam-bam da Kalu da Akpabio domin ba a rantsar da shi ba tukuna, amma shi ma yana cikin wadanda ke da tarihi a ofishin EFCC.

A 2017, jami’an EFCC sun taso tsohon Gwamnan a gaba, ana zargin an gano wasu kudin Paris Club; N500m da $500,000 a asusunsa, kotu ta ce a karbe kudin.

Babu abin da ya hada Sani Musa, Jibrin Barau da Osita Izunaso da EFCC. Babu mamaki domin a ‘yan takaran, su kadai ne ba su taba yin Gwamna ba.

Za ayi wa jam'iyyar APC bore

A rahoton da mu ka fitar a ranar Juma’a, an ji cewa akwai yiwuwar jam’iyyar APC NWC za ta canza tunani a kan batun shugabancin Majalisar Tarayya.

Boren Sanatoci da ‘Yan Majalisan Arewa zai tursasa Shugabannin APC su yi amai su lashe, alamu sun nuna watakila a canza tsarin kason kujeru da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng