Akwai Yiwuwar Messi Ya Koma Wasa a Saudi a Cinikin da Zai Girgiza Duniyar Kwallo
- Ana tunani Lionel Messi zai yi sallama da Paris Saint-Germain bayan kusan shekaru 2 a Faransa
- Alakar ‘dan wasan da kungiyarsa ya yi tsami, wasu magoya sun fara sukar ‘dan wasan Duniyar
- Al Hilal ta shiga zawarci, amma watakila tsohon Tauraron Barcelonan ba zai so zuwa Saudi ba
Paris - Rade-radi sun yi yawa a game da makomar ‘dan wasan kwallon Duniya Lionel Messi a kungiyar Paris Saint-Germain musamman a kwanaki nan.
Rahoton da aka samu daga AFP yana nuna ‘dan wasan gaban na kasar Argentina zai raba jihar da PSG, alakar da ke tsakanin su biyun ya tabarbare a yanzu.
Duk da labari ya zo cewa wata kungiyar kasar Saudi Arabiya, Al-Hilal tayi wa Lionel Messi tayin kwangilar £522m, ba tilas ba ne ayi dace cinikin ya fada.
Saudi: Inda cikas yake
Zargin da ake yi shi ne mai dakin ‘dan wasan na Duniya, Antonela Roccuzzo ba za ta yarda ya bar Turai, ya koma buga kwallon kafa a gabas ta tsakiya ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ko da Messi bai tafi kungiyar Al-Hilal ba, majiya daga wajen shahararren ‘dan jaridar nan, Fabrizio Romano ta tabbatar da cewa bana zai bar kasar Faransa.
Labarin da aka samu a L’Equipe ta hanyar Daily Mail, ya ce Antonela Roccuzzo ta nuna ba tunanin ita da Messi da yaransu uku za su iya rayuwa a Saudi.
Messi v PSG: An samu sabani
Dangantakar PSG da tsohon ‘dan wasan na Barcelona tayi tsamin da ta kai sai da aka dakatar da shi na tsawon makonni biyu saboda ya yi tafiya babu izini.
Tauraron ya kama hanya zuwa Saudi Arabiya ba tare da an ba shi dama ba, hakan ya jawo aka yi wasa da Troyes babu shi, duk da ya nemi afuwar kulob din.
Ana haka ne sai aka ji wasu magoya bayan PSG sun yi cincirindo, su na caccakar ‘dan wasan.
Daily Mail ta ce Al-Hilal ta ba ‘dan wasan na PSG kwangilar shekaru biyu tare da damar ya kara shekara ta uku idan ya yi sha’awar cigaba da zama a Asiya.
Idan Messi mai shekara 35 ya karbi tayin kwangilar, ana tunanin zai tashi da Naira biliyan 303.43, kudin da ya sha gaban abin da ake biyan Cristiano Ronaldo.
CR7 a kungiyar Al Nasr
A kudin Najeriya, kwanaki kun samu labari Cristiano Ronaldo zai rika samun dukiyar da ta haura Naira Biliyan 2 a kowane wata a gasar kwallon Saudi.
Tun a farkon 2023 aka ji Cristiano Ronaldo ya zama ‘dan wasan da ya fi kowa albashi. Tauraron ya sha gaban Lionel Messi da ‘Dan kwallon Brazil, Neymar Jr.
Asali: Legit.ng