Shekaru 7 da Suka Gabata, Wani Mutum Yayi Hasashen Nasarar Messi, Wallafarsa ta Yadu a Twitter
- Tsananin murna da annashuwa tare da shagali ya biyo bayan nasarar da Argentina ta samu a gasar kwallo ta kofin diya a ranar Lahadi, 18 ga Disamba
- Ana tsaka da hakan, wani mutum yayi suna a intanet bayan hasashen da yayi a watan Maris sin 2015 kan nasarar da Lionel Messi zai samu da tarihin da zai kafa
- Masoyin wasn kwallon kafan ya hango cewa zakaran PSG din mai shekaru 35 zai daga kofin gasar kwallon kafan a yunkurinsa na 5
Jama'a sun mika wuya tare da kwarzanta wani mutum kan hasashen da yayi na makomar Messi a gasar kwallon kafa ta kofin duniya da aka kammala a Qatar na 2022.
A wallafar da yayi a Twitter a ranar 20 ga watan Maris din 2015, Jose Miguel Polanco yayi hasashen cewa Lionel Andres Messi zai yi nasarar zama zakaran kwallon kafan da ba a taba yi ba a gasar ta duniya.
Yayin da Jose bai hango shekaru Messi daidai ba, yayi kira ga jama'a da a sake duba wallafarsa bayan shekaru bakwai masu zuwa.
Bayan Argentina tayi nasarar lallasa Faransa, wallafarsa ta yadu inda jama'a suka dinga garzayawa wurinsa neman labarin abinda zai faru a nan gaba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wallafar Jose ta hada jinjina dubu 306, sama da mutum dubu 115 suka sake wallafawa yayin da sama da dubu 71 suka tsakura daga wallafar inda suka yi tasu.
Martanin 'yan soshiyal midiya
Tuni jama'a suka fara tsokaci, ga wasu daga ciki:
@ItsDavidJ13 yace:
"Ba dole ba, yana da wallafa masu yawa inda yake ta canka amma ya goge wadanda ba daidai ba."
@1chiefowonikoko yace:
"'Dan uwa taimaka mana ka duba, Tinubu zai ci zaben 2023 ne ko Obi? Mu 'yan Najeriya zamu gode maka idan ka taimaka mana."
"Ku Wuce Ɗaki": Wani Mutumi Ya Sunkuci Matarsa Yayin da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Bidiyon Ya Ja Hankali
@optionkontrol yace:
"Wannan ne ake kira da hasashen abinda zai faru nan gaba, Manyan mutane. Yanzu za ka zama babban bokan duniya."
@NasaMcmahon yace:
"Ga wadanda suka daburce kan yadda ya samu har kwanan watan daidai, ana gobe zai yi wallafar FIFA ta sanar da cewa ranar... Daga nan ya saka kudinsa kan cewa Messi zai yi nasara...Yayi kokarin hasasen amma ba kamar yadda kuke zuzutawa ba."
Kyautukan da za a ba kasashen da suka je gasar kofin kwallon kafa na duniya
A wani labari na daban, a ranar Lahadi aka kammala gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da aka yi a kasar Qatar.
An gano cewa, FIFA ta ware makuden kudi har $440 miliyan somin kyauta gga kasashen da suka samu damar buga wasan.
Asali: Legit.ng