Wani Mutumi Ya Bata a Abuja Bayan Man United Ta Casa Arsenal

Wani Mutumi Ya Bata a Abuja Bayan Man United Ta Casa Arsenal

  • Wani masoyin ƙungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila Arsenal, ya ɓata a yankin Kubwa, FCT Abuja bayan Manchester ta casa su ranar Lahadi
  • Mazauna yankin sun bayyana yadda ya yi kurin cewa cikin sauƙi zasu zuba wa Man U kwallaye kuma ya ɗaukar musu alƙawari
  • Rashford ya zura kwallo biyu a raga a wasan wanda ya kawo ƙarshen ganiyar da Arsenaal take yi a wannan kakar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Wani Mutumi, Kingsley Ikechukwu, wanda ake kira 'IK' a taƙaice ya yi ɓatan dabo, an neme shi an rasa a yankin Kubwa dake birnin Tarayya Abuja bayan wasan tamaula tsakanin Manchester United da Arsenal.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Ikechukwu, ɗan gani kashenin ƙungiyar Arsenal, ya yi kurarin cewa ƙungiyar da yake goyon baya zata lallasa Man United.

Kara karanta wannan

Tsoho Ministan Ya Fallasa Wani Sirri, Ya Faɗi Abu Ɗaya Da Zai Sa Yan Najeriya Su Zaɓi APC a 2023

Wasan Man U da Arsenal.
Wani Mutumi Ya Bata a Abuja Bayan Man United Ta Casa Arsenal Hoto: Man United/facebook
Asali: Facebook

A wasan, ɗan wasan gaba, Marcus Rashford, ya zura kwallaye biyu a raga yayin da Man United ta yi nasara a wasanni huɗu a jere kuma ta kawo karshen ganiyar da Arsenal ke yi tun farkon fara kakar wasan 2022/2023 a Premier na ƙasar Ingila.

Meyasa mutumin ya ɓata?

Wani mazaunin yankin, Adeleye Tunde, yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kasancewarsa ɗan gani kashenin Arsenal tun lokacin Koci, Arsene Wenger, ya mana alƙawarin saya mana kayan shaye-shaye, inda ya yi ikirarin cewa zasu casa Manchester United cikin sauki a filin wasan Old Trafford."

"Muna da yaƙinin bayan wani ɗan lokaci IK zai dawo da kansa kuma ba zamu yi ƙasa a guiwa ba wajen tambayarsa kayan shan da ya mana alƙawari domin alƙawari bashi ne," inji wani mazauni na daban mai suna Benson.

Yayin da wakilin jaridar ya ziyarci yankin ranar Litinin, an shaida masa babu wanda ya kai rahoton ɓatan IK wurin 'yan sanda domin ana fatan zai dawo gida da kafarsa, mai yuwuwa ci ne ya masa zafi.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Wurin Taron Jam'iyyar Siyasa, Sun Aikata Ɓarna

A wani labarin kuma Shahararren ‘Dan Kwallon kafan Najeriya Ya Koma Jami’a, Yana Neman Ilmin Digiri

‘Dan wasan Super Eagles, Wilfred Ndidi ya kammala wani kwas da yake yi domin samun kwarewar kasuwanci a jami’ar Birtaniya.

Wilfred Ndidi ya samu shaidar karatu daga De Montfort University a Leicester wanda za ta ba shi damar yin digiri da digir-gir.

Asali: Legit.ng

Online view pixel