Ahmed Musa ya wallafa sako mai ratsa zuciya bayan fitar Najeriya daga AFCON

Ahmed Musa ya wallafa sako mai ratsa zuciya bayan fitar Najeriya daga AFCON

  • Musa Ahmed, kyaftin din kungiyar Super Eagles ya aike wa yan Najeriya da sako bayan ficewarsu daga gasar AFCON bayan shan kaye hannun Morocco
  • Ahmed ya bayyana cewa sun yi iya kokarinsu don ganin sun samu nasara amma hakan bai yiwu ba kuma haka rayuwa ta ke, amma ya ce ba za su karaya ba kuma za su dage fiye da hakan a gaba
  • Hakazalika, dan wasan Najeriya Alex Iwobi shima ya yi magana inda ya bawa 'yan Najeriya hakuri shima ya ce tabbas gaba za su jajirce don ganin sun yi nasara

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, Ahmed Musa, a karon farko ya yi magana bayan rashin nasarar da Najeriya ta yi a wasanta da Tunisia wanda hakan yasa ta fice daga gasar.

Kara karanta wannan

Buhari: Ka da 'Yan Najeriya su cire tsammani daga Super Eagles

Yan Najeriya da dama sun rika tofa albarkacin bakinsu game da yan wasan da Super Eagles bayan rashin nasarar da suka yi a wasarsu daTunisia a ranar Lahadi

Ahmed Musa ya wallafa sako mai ratsa zuciya bayan fitar Najeriya daga AFCON
A karon farko, Ahmed Musa ya magantu bayan fitar Najeriya daga AFCON. Hoto: @ahmedmusa718
Asali: Twitter

Ahmed Musa ya wallafa rubutu a shafinsa na Twitter a ranar Talata 25 ga watan Janairu inda ya yi magana game da gasar yana mai cewa haka rayuwa ta ke, ba komai da mutum ke so ya ke samu ba amma dai sun yi iya kokarinsu, kuma za su kara dagewa a gaba.

Kalamansa:

"A rayuwa, ba kowanne lokaci bane muke samuna abin da muke so kuma wannan lamari ne da ya kamata mu yarda da shi komin zafinsa. Mun yi kokarin mu dari bisa dari, amma kokarin bai isa bamu nasara ba.

Kara karanta wannan

Ustazai: Wankan kamala na amarya da ango a wajen liyafar aurensu ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta

"Ba za mu karaya ba, za mu jajirce fiye da hakan a gaba. Mun gode da goyon bayanku da addu'oi."

"Ba mu kyauta wa magoya bayan mu ba' - Iwobi ya ce bayan fitar Super Eagles daga AFCON

Hakazalika, dan wasan Najeriya mai buga tsakiya, Alex Iwobi shima ya wallafa sako a dandalin sada zumunta yana bawa magoya bayansa hakuri kan cire su daga AFCON.

Bayan kammala wasan, wasu magoya baya sun rika nuna bacin ransu a dandalin sada zumunta suna cewa laifin Iwobi ne da Okoye.

An jingina wa Iwobi laifi saboda samun jan kati a minti 66 na wasan yayin da ya taka Youssef Mskani a idon sahunsa na dama.

Kalamai na suka da ake yi masa a shafinsa na Instagram yasa ya rufe sashin da mutane ke wallafa ra'ayoyinsu.

Amma a wani rubutu da ya yi a Twitter a ranar Talata, Iwobi ya amsa cewa ba a kyauta wa magoya bayansu a Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Ban yi wa Buhari kamfen ba, hotunansa kawai na wallafa, Dele Momodu

Ya kuma yi alkawarin nan gaba tawagar za ta kara dagewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164