Siyasar Najeriya: Babban hadimin gwamna ya koma jam'iyyar hamayya PDP
- Awanni 48 kacal kafin fafata zaɓen gwamnan jihar Anambra, hadimin gwamna Obiano ya koma jam'iyyar PDP
- Mai baiwa gwamna shawara ta musamman, Tommy Okoli, yace ya koma PDP ne domin ɗan takarar ta ne zai iya ceto jihar Anambra
- A ranar Asabar mai zuwa 6 ga watan Nuwamba, hukumar zaɓe mai zaman kanta zata gudanar da zaɓen gwamna a jihar Anambra
Anambra - Yayin da ake gab da fita fafatawa zaɓen gwamnan jihar Anambra, mai baiwa gwamna Willie Obiano shawara ta musamman, Tommy Okoli, ya koma jam'iyyar hamayya PDP.
Punch tace hadimin gwamnan, wanda tsohon ɗan takarar gwamnan jihar ne karkashin jam'iyya mai mulki, APGA, ya sanar da sauya shekarsa ne ranar Alhamis.
Okoli, ya bayyana matakin komawa PDP ne a wurin gangamin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar PDP da ya gudana a Ukpor, karamar hukumar Nnewi South.
Shin dagaske kasurgumin dan bindigan da ya addabi Arewa, Dogo Gide, ya mutu? Gaskiyar abinda ya faru
A cewarsa yana goyon bayan ɗan takarar da PDP ta tsayar, Valentine Ozigbo, da mataimakinsa, Azuka Enemo, a zaɓen dake tafe ranar Asabar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ƙara da cewa zai bada gudummuwa iyakar karfinsa wajen ganin Ozigbo ya samu nasara, bayan binciken yan takara baki ɗaya kuma ya gano PDP ce ta fi dacewa da ceto Anambra.
Ko meyasa ya fice daga APGA?
Okoli ya bayyana cewa sai da ya gana da mutanen mazaɓarsa, waɗan da suka tabbatar masa amincewarsu ya koma PDP.
The Nation ta ruwaito A jawabinsa yace:
"Na yanke hukuncin goyon bayan yan takarar gwamnan Anambra karkashin PDP, Valentine Ozigbo da Azuka Enemuo a zaben dake tafe ranar 6 ga watan Nuwamba."
"Zan yi amfani da dukiyata, mutane na da kuma duk abinda nake da shi wajen taimaka wa takarar su."
"Na ɗauki wannan matakin mai wahala bayan tattaunawa da mutane na da tawagar yaƙin neman zaɓe, saboda haka ina rokon mambobin wannan jam'iyyar su zabi Valentine Ozigbo."
Okoli ya gode wa gwamna Obiano
Daga nan kuma Okoli ya gode wa gwamnan Anambra, Willie Obiano, bisa damar da ya bashi na yin aiki a gwamnatinsa lokacin yana APGA.
"Ina mai tabbatar da ficewa ta daga jam'iyyar APGA. Ina miƙa tsantsar godiya ta ga Gwamna Obiano bisa damar da ya bani na yin aiki a gwamnatinsa."
A wani labarin kuma Dubbannin mambobin jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa Jam'iyyar PDP a jihar Cross Ribas
Shugaban jam'iyyar hamayya PDP reshen jihar Cross Ribas, Venatius Ikem, ya karbi masu sauya sheƙa sama da mutun 5,000 daga APC zuwa PDP.
Vanguard ta ruwaito cewa PDP ta shirya taron karɓar dubbannin masu sauya shekan ne a kwalejin fasaha dake Ogoja.
Asali: Legit.ng