Jerin wasanni 6 da aka ragargaza wa Manchester United kwallaye a Tarihin Premier
- A karon farko Liverpool ta lallasa Manchester United da ci 5 babu ko ɗaya, wasan da ya kafa sabon tarihi a fagen tamaula
- Ɗan wasan tsakiyar Man United, Paul Pogba ya karbi jan kati a wasan, yayin da Salah ya jefa kwallaye uku rigis
- Wannan ba shi ne na farko da ƙungiyar ta sha mugun kaye ba, amma dai a hannun Liverpool shine na farko
Manchester, United Kingdom - A fagen wasan kwallon kafa, wasan da Manchester United ta sha kashi a hannun Liverpool da ci 5 ya ja hankalin ma'abota kwallon kafa na duniya.
Duk da tarihi ya nuna cewa wannan ba shi ne karon farko da ƙungiyar ta kwashi kashinta a hannu ba, amma BBC Hausa ta rahoto cewa shine na farko da ta ji ba daɗi da kwallaye da yawa a hannun Liverpool.
Jerin Sunaye: Shugabannin Ƴan Ta’adda da Ƴan Bindiga Da Aka Kashe Daga Farkon Shekarar 2021 Zuwa Yanzu
Wasan wanda aka fafata a filin wasa na Old Trafford, Keita ne ya fara jefa kwallo a raga, sai kuma Jota ya ƙara ta biyu, kafin Muhammed Salah ya jefa kwallaye uku rigis.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasanni 6 da Man United ta sha kwallaye a gasar Premiel League ta ƙasar Ingila.
1. Newcastle United 5 - 0 Manchester United
Kungiyar Newcastle ta kawo cikas a kokarin Man United na lashe gasar Premier a shekarar 1996, lokacin da ta zuba mata kwallaye biyar rigis a raga.
Duk da kasancewar mai tsaron ragar United a wancan lokacin, Schmeichel, yana tashe amma ita kuma Newcastle na da yan wasan gaba dake haskawa.
Alan Shearer, Darren Peacock da Les Ferdinand na cikin tawagar yan wasan Newcastle dake haskawa a wancan lokacin.
2. Southampton 6 - 3 Manchester United
Man United ta sake shan kwallaye a hannun Southampton da ci 6-3 mako ɗaya tal bayan Newcastle ta casa ta.
Dan wasan gaba Egil Ostentad, shine ya jefa kwallo uku, Eyal Berkovic, ya jefa guda biyu sannan Matt Le Tissier ya ci ɗaya, bayan kaftin ɗin United Roy Keane ya karbi jan kati.
3. Chelsea 5 - 0 Manchester United
Hakanan kuma shekarar 1999 da Manchester United ta lashe gasar zakarun nahiyar turai, kungiyar ta sha kashi da kwallaye 5 a hannun Chelsea.
Ɗan wasan United mai taka leda daga tsakiya Nicky But ya karbi katin kora daga filin wasa.
4. Manchester United 1 - 4 Liverpool
A shekarar 2009, Liverpool ta zazzaga wa Manchester kwallo 4 har gida ta hannun zaratan yan wasanta Torres, Gerrard, Aurelio da kuma Dossena.
Hakanan a wannan wasa zakakurin ɗan bayan United, Nemanja Vidic ya karbi jan kati a wasan, amma duk da haka United ce ta lashe gasar a shekarar.
5. Manchester United 1 - 6 Manchester City
Makociyar United, Manchester City ta kafa wa kungiyar sabon tarihi na zura mata kwallo 6 har gida tun bayan shekarar 1930.
Yan wasan City Mario Balotelli, Edin Dzeko, Kun Aguero da David Silva ne suka jefa kwallaye a ragar United a shekarar 2011, wanda har yanzun ake kiran wasan da "Six in the city."
6. Manchester United 1 - 6 Tottenham
A Shekarar da ta gabata 2020, Tottenham ta suburbuɗa kwallo shida rigis a ragar Manchester United har gida bayan ɗan wasa Anthony Martial ya karbi jan kati.
United ta fara wasan da sa'a inda ɗan wasanta Bruno Fernandez ya fara jefa kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga, kafin jan kati ya canza wasan.
Harry Kane da Son sun jefa kwallaye biyu kowannensu, sai kuma Tanguy Ndombele da Sergie Aurier suka ci nasu kwallon.
A wani labarin kuma Mourinho ya sha mummunan kashi a hannun karamin kulob, an dirka masa kwallaye 6
A ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, 2021, kungiyar Bodo/Glimt ta doke AS Roma ta kasar Italiya a gasar Europa Conference League.
Jose Mourinho ya yarda ya dauki nauyin wannan kashi da kungiyar da yake horaswa ta sha a matsayinsa na kocin ‘yan wasan.
Asali: Legit.ng